Jonathan ne ya hana ceto 'yan Chibok — Birtaniya

Wasu daga cikin 'yan matan Chibok da suka kubuta
Image caption An dade dai ana zargin gwamnatin da ta gabata da yin sakaci, wajen kubuto da 'yan matan

Rahotanni sun ce tsohon Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya yi watsi da bukatar Birtaniya ta tallafa wa kasar wurin ceto 'yan matan Chibok jim kadan bayan sace su.

Jaridar The Guardian ta Birtaniya ta ce ta samu takardun da suka nuna an yi wata tattaunawa a Abuja a watan Satumbar 2014, tsakanin mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan harkokin tsaro, da tsohon mataimakin Sakataren Harkokin wajen Birtaniya James Duggrige, inda suka tattauna kan matakan da za a dauka don ceto 'yan matan.

Jaridar ta jaddada cewa har yanzu sauran 'yan matan 195 na hannun mayakan, wadanda aka kubutar da wadanda suka tsero sun bayyana rayuwar kunci da azabar da suka fuskanta a lokacin da suke hannun 'yan Boko Haram.

A watan Afrilun 2014 ne mayakan Boko Haram suka sace 'yan matan sama da 200 daga dakunan kwanansu a garin Chibok, kuma har yanzu mafi yawansu na hannun kungiyar.

Kawo yanzu babu wani martani daga Mista Jonathan ko jami'an tsohuwar gwamnatinsa, kuma yunkurinmu na ji daga wurinsu bai kai ga nasara ba kawo yanzu.

Sai dai Ministan yada labaran Najeriya Alhaji Lai Muhammad ya ce wannan rahoto ya kara tabbatar da korafin gwamnati mai ci, na cewa gwamnatin Shugaba Jonathan ba ta dauki matakan da suka dace dan kubuto da 'yan matan ba.

Ya shaida wa BBC cewa "dama mun sha fada cewa gwamnatin PDP siyasa ta siyasantar da irikicin na Boko Haram ne kawai maimakon daukar matakan ceto rayukan al'ummar kasar".

Ya kara da cewa za su zauna domin tattauna wannan batu don sanin matakin da ya kamata a dauka nan gaba.

Labarai masu alaka