Nigeria: Gwamnatin jihar Kaduna za ta sayar da gidaje 2000 na ma'aikata

Kaduna Hakkin mallakar hoto Kaduna state goverment
Image caption Dubban ma'aikata da iyalansu ka iya rasa muhallai a jihar Kaduna

Takaddama ta barke tsakanin gwamnatin jihar Kaduna a Najeriya da kungiyar kwadago ta NLC game da shirin gwamnati na sayar da wasu gidaje 2000 da ma'aikata ke zaune a cikinsu.

Kungiyar kwadagon ta NLC ta nuna damuwa a bisa shirin gwamnatin jahar ta Kaduna na yin gwanjon gidajen ne ga masu halin saya, imma ma'aikata ko kuma 'yan kasuwa.

Ta ce ta dauki matakin ne domin rage kashe kudi da gwamnati ke yi wajen kula da gidajen, amma kungiyar kwadagon na cewa gwamnatin wadda Malam Nasir el-Rufai ke jagoranta, na shirin yi wa ma'aikatan kora da hali ne domin galibin ma'aikatan basu da karfin sayan gidajen, kuma ba su da inda za su zauna idan aka fidda su daga gidajen.

Shugaban kungiyar NLC a jihar Kaduna, Kwamaret Adamu Ango, ya shaida wa BBC cewa ya kamata a bar ma'aikata a cikin gidajen domin hakan zai taimaka masu wajen gudanar da aiki yadda ya kamata, amma fitar da ma'aikata marasa karfin sayan gidajen za yi illa ga kwazonsu da kuma jefa cikin kuncin rayuwa.

Ya kara da cewa bisa kiyasi, ko wane gida zai iya kaiwa naira muliyan goma zuwa naira muliyan ashirin, abin da ya ce ya fi karfin galibin ma'aikata dake cikin gidajen.

Rahotanni na cewa gidajen na gwamnati kimanin dubu biyu da ake shirin sayarwa suna yankuna daban-daban ne a jihar, kuma gwamnatocin da suka gabata ne suka gina su domin rage wa ma'aikata wahalar samun muhalli a inda aka kai su aiki.

Gwamnatin jihar ta Kaduna dai ta ce nan ba da dadewa ba ne za ta yi gwanjon gidajen ga masu kudin da za su iya saya, kuma su ma ma'aikata na da damar gabatar da bukatarsu ta sayan gidajen da suke ciki domin su mallaka.

Ta kuma kara da cewa za ta sayar da gidajen ne domin rage dawainiyar da ta ke yi wajen kula da gidajen musamman gyare-gyare da akan yi daga lokaci zuwa lokaci.

Wasu kananan ma'aikata da lamarin zai shafa sun shaida wa BBC cewa kamata ya yi gwamnan jihar ta Kaduna Malam Nasiru el-Rufai ya tausaya masu a wannan yunkuri da gwamnatinsa ke yi.

Wakilin BBC Nurah Mohammed Ringim ya ruwaito cewa gwamnatin jihar Kaduna ta sha musanta zargin da wasu ke yi cewa tana shirin korar ma'aikatan gwamnati daga gidajen ne domin mallaka wa wasu 'yan siyasa da 'yan kasuwa dake kusa da ita.