Majalisar Amurka za ta binciki Obama

Image caption Trump da Obama ba su jituwa kan batutuwa da dama

Fadar gwamnatin Amurka ta White House ta bukaci Majalisar Wakilan Amurka ta bincika domin gano ko gwamnatin Barack Obama da ta shude ta yi amfani da ikonta ta hanyar da ba ta dace ba a lokacin yakin neman zaben shugaban kasar da aka yi a bara.

Matakin ya biyo bayan zarge-zargen da shugaban kasar na yanzu, Mista Donald Trump, ya yi ne cewa an yi satar tatsar bayanan sadarwar wayoyinsa gabanin zaben.

Wata sanarwa daga fadar gwamnatin Amurka ta ce rahotanni dake nuni da cewa gwamnatin kasar da ta gabata, ta yi bincike da kuma ayyukan sa ido masu nasaba da manufa ta siyasa, wani abin damuwa ne matuka.

Shugaba Donald Trump ya bukaci kwamitin bayanan sirri na majalisar wakilai wanda ke binciken zargin hannun Rasha a zaben na Amurka da ya fadada binciken nasa.

A jiya dai wani mai magana da yawun Mista Obama ya ce tsohon shugaban bai taba bayar da umarnin yi wa wani dan Amurka leken asiri ba.

A karkashin dokokin Amurka, dalili daya ne zai sa a bayar da izinin satar tatsar bayanan wayoyin mutum. Dalilin kuma shi ne idan akwai wata hujjar da zata sa a yi imanin cewa mutumin dan koren wata kasar waje ne.