Limamin coci ya yi wa yarinya fyade ta haihu

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Limaman katolika a sassa daban-daban na duniya na yawan fuskantar zargin lalata da kananan yara

'Yan sanda a kudancin Indiya sun ce suna farautar wasu mata shida masu yi wa majami'ar Katolika hidima, wadanda ake zargi da yin rufa-rufa game da haihuwar da wata karamar yarinya da bata kai shekarun aure ba ta yi.

Har ila yau 'yan-sanda na yi wa limanin majami'arsu tambayoyi bisa zargin shi ya yi wa yarinyar ciki.

A makon jiya aka kama limanin na majami'ar Katolika a jihar Kerala bisa zargin shi ne ya yi wa yarinyar mai shekara goma sha bakwai, fyade ta yi ciki.

Yarinyar da lamarin ya rutsa da ita daliba ce a wata makarantar cocin.

'Yan sanda na zargin mata masu yi wa majami'ar hidima wadanda biyu daga cikinsu likitoci ne, sun boye haihuwar kana suka kai jaririn wani gidan marayu na majami'ar.

A watan jiya ne yarinyar ta haihu.

A kasar Indiya ana daukar tarawa da 'yarinyar da bata kai shekaru goma sha takwas ba a matsayin fyade.

Wata kungiyar fafutikar kare hakkin yara ce ta ankarar da 'yan sanda kan abin kunyar da ake zargin ya faru.