'Da ma mun fada Jonathan bai so ceto 'yan Chibok ba'

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Shugaba Buhari dai ya yi alkawarin ceto 'yan matan Chibok

Gwamnatin Najeriya ta ce ba ta yi mamaki ba kan rahotannin da ke nuna yadda tsohuwar gwamnatin kasar ta nuna halin ko-in-kula wajen ceto 'yan matan Chibok.

Jaridar The Guardian ta Birtaniya dai ta ce tsohon Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya yi watsi da bukatar Birtaniya ta tallafa wa kasar wurin ceto 'yan matan Chibok, jim kadan bayan sace su.

Jaridar ta ce ta samu wasu takardu da suka nuna gudanar da wata tattaunawa a Abuja, a watan Satumbar 2014, tsakanin mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan harkokin tsaro, da tsohon mataimakin Sakataren Harkokin wajen Birtaniya James Duggrige, inda suka tattauna kan matakan da za a dauka don ceto 'yan matan.

Jaridar ta jaddada cewa har yanzu sauran 'yan matan 195 na hannun mayakan, wadanda aka kubutar da wadanda suka tsero sun bayyana rayuwar kunci da azabar da suka fuskanta a lokacin da suke hannun 'yan Boko Haram.

Ministan yada labaran Najeriya, Alhaji Lai Muhammad ya ce ba su yi mamakin rahoton jaridar ba bisa la'akari da yadda gwamnatin da ta shude ta sanya siyasa a batun.

Ya ce "Ka da amanta fa sai da aka kwashe kwanaki kimanin 15 kafin gwamnatin Jonathan ma ta amince da cewa an sace 'yan matan nan."

Dangane da shafa wa gwamnatin Buhari kashin kaji wajen gaza ceto 'yan matan na Chibok, mista Lai ya ce "Wannan ai maganar banza ce ka da amanta fa an kwashe kusan kwanaki 400 tsakanin sace 'yan matan da hawanmu gwamnati."

Lai Muhammad ya kara da cewa a shirye gwamnatinsu take ta hada hannu da duk mai son ceto 'yan matan.

A watan Afrilun 2014 ne mayakan Boko Haram suka sace 'yan matan sama da 200 daga dakunan kwanansu a makarantar sakandiren garin Chibok, kuma har yanzu mafi yawansu na hannun kungiyar.

Kawo yanzu dai babu wani martani daga Mista Jonathan ko jami'an tsohuwar gwamnatin nasa.