'Yan Nijar na yi wa Buhari addu'ar neman sauki

'Yan Nijar mazauna Najeriya na yiwa shugaban kasar fatan samun lafiya
Bayanan hoto,

'Yan Nijar mazauna Najeriya na yiwa shugaban kasar fatan samun lafiya

Al'ummar Nijar mazauna Najeriya sun wa shugaba Muhammadu Buhari addu'o'in neman lafiya, a birnin Legas.

A yayin addu'ar, mahalarta wadanda suka hada da manyan malamai da sauran mutane sun sauke Alqur'ani mai tsarki kan lafiyar shugaban da nema wa kasashen biyu zaman lafiya da bunkasar arziki.

'Yan Nijar din sun ce sun yi addu'o'in ne saboda duk abin da ya shafi Najeriya ya taba Nijar.

Wannan dai ba shi ne karon farko da ake gudanar da irin wadannan addu'o'i ba na nema wa shugaba Buhari sauki , ko a kwanakin baya an gudanar da makamanciyar wannan addu'ar a jihohin Kano da Borno.

Sannan kuma kiristoci ma suna gudanar da irin wadannan addu'o'in ga shugaban.