'Yan bindiga sun kashe sojoji 11 a Mali

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Akwai dai kungiyoyin 'yan bindiga da dama a Mali

Masu tayar da kayar baya a arewacin Mali sun kai hari kan wani sansanin soji a kusa da iyakar kasar da Burkina Faso lamarin da ya yi sanadin mutuwar sojoji goma sha daya.

Akwai dai kungiyoyin 'yan tawaye da dama a wannan yanki, kuma har yanzu ba a kai ga gano wadanda suka kai harin ba.

Wani ganau ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa cewa maharan sun yi awon gaba da makaman sojojin da dama.

A wani labarin kuma, rahotannni daga birnin Timbuktu na cewa wasu 'yan bindiga sun kewaye tare da toshe hanyar shiga da fita daga birnin, sakamakon kin amincewa da jami'an gwamnatin da aka nada.

Labarai masu alaka