Shafukan sada zumunta 'na daɗa haifar da kaɗaici'

Lonely man Hakkin mallakar hoto Science Photo Library

Masana halayyar dan adam na Amurka sun gano cewa shafukan sada zumunta irin su Twitter da Facebook da Pinterest na haddasa wa mutane da yawa jin kadaici.

Rahoton ya gano cewa sama da sa'o'i biyu da mutane ke yi suna amfani da shafukan sada zumunta a rana, yana ninka dabi'ar sanya da mutum ya kebe kansa daga jama'a.

Rahoton ya yi amanna cewar irin yadda mutane ke baje kolin hotunansu a shafukan sada zumuntar na yadda rayuwarsu take, yana sa wasu da basu da irin wannan tagomashin jin kyashi da hassada.

Har ila yau binciken ya yi duba ga wadanda suke amfani da shafukan Instagram da Snapchat da kuma Tumblr.

Daya daga cikin wadanda suka wallafa rahoton, kuma Farfesa a fannin lafiyar yara da ke Jami'ar Pittsburgh, Elizabeth Miller ta ce, "Ba mu da masaniyar wanda ya fara zuwa, tsakanin amfani da shafukan sada zumunta da kuma kauracewa jama'a da mutane ke yi don karan kansu."

Zai iya yiyuwa matasan da ada suka kauracewa jama'a ne suka koma yin amfani da shafukan sada zumunta na zamani. Ko kuma zai iya kasancewa yawan amfanin da suke yi da shafukan sada zumuntar ne ya jawo suke kauracewa sauran mutane," in ji ta.

Bayanin da aka yi a rahoton ya nuna cewa yawan lokacin da mutane ke batawa a yanar gizo wajen amfani da shafukan sada zumunta, to hakan zai sa su kasance ba su da lokacin mutane da ke kusa da su.

Har ila yau, amfani da shafukan yana kara sa jin wariya, kamar ganin hotunan yadda abokai suke shagalinsu a wani taro da suka halarta, wanda su ba a gayyace su ba.

Tawagar masu binciken ta ji ta bakin kusan matasa 2,000 masu shekaru daga 19 zuwa 32, kan yada suke amfani da shafukan sada zumuntar.

Hattara da shafukan sada zumunta. Kar ka yi asarar aikinka

Farfesa Brian Primack na Jami'ar Pittsburgh a bangaren koyon kiwon lafiya, ya ce, "Wannan batu ne mai matukar muhimmanci da za a yi nazari akansa saboda yadda matsalolin da suka shafi lafiyar kwakwalwa da yadda mutane da kebe kansu daga jama'a suka zama annoba a tsakanin matasa."

"Tun fil azal mu ma'abota walwala ne, sai dai kuma zamani ya zo da abin da yake raba kawunanmu maimakon ya kara hada kanmu.

"A yayin da shafukan sada zumunta na zamani zai ba da damar cike gurbin da aka bari na kauracewa daga jama'a, wannan nazari ya nuna cewa ba lallai ne hakan ya zama mafita ga mutane ba."

Labarai masu alaka