Cinikin naman jakuna zuwa China na bunkasa a Kenya

fatunan jakuna shanye a mayankar Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ana fitar da naman jakunan ne zuwa kasar China,yayin da aka hana sayar da shi a kasuwannin kasar

Mayankar mai suna Goldox Slaughterhouse wadda mallakin wani dan kasar China ne mai suna Lu Donglin, an bude ta ne a yammacin garin Baringo a watan Afrilun shekarar da ta gabata bayan da gwamnatin kasar ta amince da amfani naman jakuna a hukumance.

Ana fitar da naman jakunan ne zuwa kasar China, yayin da aka hana sayar da shi a kasuwannin kasar.

Jaridar Daily Nation ta bayar da rahoton cewa ana yanka a kalla jakuna 600 a kowacce rana a mayankar.

Mista Donglin ya ce suna bin dokoki masu tsauri, inda suke biyan dala 77 a kan ko wanne jaki.

"Mun dogara da wadanda suke kawo mana jakuna daga kasar Tanzaniya da Turkiyya da Trans Mara da kuma Maralal," in ji shi.

Kasuwancin fatar jakunan na kawo miliyoyin daloli, tana kuma da amfani mai tarin yawa ga kasar China wadda ke hada magunguna ita.

Ana amfani da sinadarin gelatine wanda ke jikin fatar jakunan domin hada wasu magunguna.

Wasu kuma na ganin cewa sinadarin ya kan taimaka wajen rage matsalar da mata ke fuskanta idan suka kai munzalin da jinin haila ya dauke musu.

Haka kuma ana amfani da fatar wajen magance matsalar barci.

Labarai masu alaka