Me ya sa North Korea ke haifar da ce-ce-kuce?

Kasashen duniya sun yi alawadai da harba makaman da Koriya ta Arewa ta yi Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Kasashen duniya sun yi alawadai da harba makaman da Koriya ta Arewa ta yi

Koriya ta Arewa ta bayyana cewa harba makamai masu linzami da ta yi a ranar Litinin atisaye ne ba wani ta nufa ba, sai dai lamarin na kara haifar da ce-ce-kuce.

Wata kafar yada labaran kasar ta bayyana cewa shugaban kasar,Kim Jong-un ya kai ziyara wajen da aka harba makaman kuma an yi komai a kan idansa.

Harba makaman da kasar ta yi ya samu suka daga kasashen duniya da dama.

Tuni dai Amurka da Japan suka bukaci a gudanar da taron gaggawa tare da kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya.

Rundunar sojin Koriya ta Kudu ta ce an harba makaman ne daga wani sansani da ke kusa da iyakar Koriya ta arewan da China.

Labarai masu alaka