Wasu 'yan bindiga sun kashe 'yan sanda a jamhuriyar Nijar

An sha kai wa jami'an tsaro hari a Nijar
Image caption An sha kai wa jami'an tsaro hari a Nijar

An kashe jami'an 'yan sanda guda biyar a jamhurioyar Nijar, bayan wani hari da ake zargin masu kaifin kishin Islama sun kai a yammacin kasar.

Mahukunta sun ce lamarin ya faru ne a garin Wanzarbe da ke kusa da iyakar kasar da Mali.

A ranar Asabar din da ta gabata ne dai gwamnatin Nijar ta ayyana dokar ta baci a wasu iyakokin kasar bakwai, bayan masu tayar da kayar baya da ke yankunan sun kaddamar da wasu hare-hare.

A watan da ya gabata ne Niger din da Mali da Chadi da Burkina Faso da kuma Mauritania, suka amince da kafa rundunar hadin gwiwa a yankin Sahel domin tabbatar da tsaro a yankunan kasashen.

Wannan na zuwa ne a dai-dai lokacin da jamhuriyar ta Niger ke fuskantar kalubalen tsaro daga kungiyar Boko Haram musamman a yankin Diffa.

Labarai masu alaka