Shin tsoffin gwamnoni nawa EFCC ta kai kotu?

Hukumar EFCC Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Kusan dukkan gwamnonin hukumar EFCC ce ke tuhumarsu

A ranar Litinin ne tsohon Gwamnan jihar Adamawa a Najeriya James Bala Ingilari ya zamo tsohon gwamna na biyu a tarihi da aka daure kan aikata laifukan da suka shafi cin hanci da rashawa.

Sai dai akwai tsaffin gwamnoni da dama da ke fuskantar shari'a kan batun cin hanci da rashawa ba, abin da kusan dukkansu suka sha musantawa.

To ko su nawa ne kawo yanzu da suke gaban kotu amma har yanzu ba a kai ga yanke musu hukunci ba.

Joshua Dariye

Tsaohon Gwamnan jihar Filato Joshua Dariye ya mulki daga shekarar 1999 zuwa 2006 bayan da aka tsige shi sakamakon zargin almundahana.

A shekarar 2007 ne hukumar da ke yaki da cin hanci ta EFCC ta tuhume shi da laifuka 23 da suka hada da halatta kudin haram da karkatar da kusan naira biliyan 1.126 mallakin gwamnatin jihar zuwa aljihunsa.

EFCC ta gurfanar da shi a gaban wata kotu a Abuja, inda ya musanta zargin da ake masa.

An yi ta jan shari'ar dai inda har Mista Dariye ya daukaka kara. Har yanzu dai ba a kammala shari'ar tasa ba, kuma mamba ne a majalisar dattawan kasar.

Boni Haruna

Boni Haruna ya mulki jihar Adamawa a Arewa maso Yammacin kasar daga 1999 zuwa shekarar 2007.

A 2008 ne hukumar EFCC ta gurfanar da shi gaban kuliya, bisa zarginsa da yin sama da fadi da dukiyar gwamnati.

An tuhume shi da aikata laifuka 21 da suka shafi almundahana.

Sai dai a watan Janairun 2014 babbar kotun da ke Adamawa ta wanke shi daga zargin da ake masa din.

Sule Lamido

Image caption Sule Lamido ya gurfana ne gaban kotu ne tare da 'ya'yansa

Tsohon gwamnan Jigawa da ya yi shekara takwas yana mulki, shi ma na fuskantar tuhuma daga hukumar EFCC, inda ta gurfanar da shi a gaban kuliya bisa zargin sa da yin sama-da-faɗi da makuden kudade.

Rahotanni sun nuna cewa Sule Lamido da 'ya'yansa sun yi cuwa-cuwar sama da N1.3 bn daga kudin gwamatin Jigawa, lamarin da suka musunta.

Daga bisani dai sai da tsohon gwamnan ya yi zaman gidan kaso na dan lokaci kafin a bayar da belin sa. Har yanzu dai ba a kammala shari'ar tasa ba.

Ihedi Ohakim

Mista Ihedi Ohakim ya zama gwamnan jihar Imo a shekarar 2007.

Kuma a watan Yulin 2015 ne EFCC ta gurfanar da shi a gaban kotu bisa zarginsa da biyan kudi lakadan kimanin naira miliyan 270, da nufin sayen gida a gundumar Asokoro da ke babban birnin kasar, Abuja.

Yawan kudin ya zarta adadin da aka yarda wani mutum ya biya wani ciniki lakadan da su, kamar yadda doka ta tanada, abin da ya musanta.

Ana kuma zarginsa da kin bayyana kadarorin da ya mallaka ga hukumar. Sai dai daga bisani kotu ta bayar da belinsa, amma an ci gaba da shari'ar.

Attahiru Bafarawa

A watan Disambar 2015 EFCC ta tuhumi tsohon gwamnan jihar Sokoto, Attahiru Dalhatu Bafarawa, da laifukan da suka danganci almundahana da halasta kudaden haramun a gaban kotu.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Shugaba Muhammadu Buhari ya sha alwashin yakar cin hanci da rashawa

EFCC dai ta kama shi ne tare da sauran wasu mutanen bisa zargin karkatar da kudade fiye da N2.1bn wadanda ke cikin kudaden da aka ware domin sayen makaman da za a yi amfani da su wajen yaki da kungiyar Boko Haram.

Duka Bafarawa da sauran mutanen sun musanta zargin da aka yi musu.

Kuma har yanzu dai ba a kammala shari'ar tasu ba.

Saminu Turaki

Shi ma Saminu Turaki, wanda ya yi mulkin jihar Jigawa na tsawon shekara takwas daga shekarar 1999 zuwa 2007 yana fuskantar tuhuma daga EFCC kan zarginsa da wawure naira biliyan 36 a lokacin da yake kan mulki.

An fara gurfanar da shi a gaban babbar kotun birnin tarayya da ke Abuja a shekarar 2007, inda aka tuhume shi da laifuka 32 masu alaka da cin hanci.

Daga baya an mayar da shari'ar babbar kotun jihar Jigawa da ke Dutse bayan da ya kalubalanci shari'ar da ake yi a kotun Abujar.

Murtala Nyako

Image caption Ana tuhumar Murtala Nyako tare da dansa Sanata Abdulaziz Nyako

An gurfanar da Tsohon Gwamnan jihar Adamawa Murtala Nyako, kan zargin sa da almundahanar naira biliyan 29.

Nyako ya zama gwamnan Adamawa a shekarar 2007, amma daga bisani aka soke zaben nasa.

Laifukan da ake tuhumar sa da su sun hada da hada kai don a yi zamba, da bushasha da kudin gwamnati da kuma bude asusun ajiya daban-daban.

Sai dai Nyako ya musanta zargin da ake masa a kotun. Har yanzu ba a kammala shari'ar ba.

Lucky Igbinedion

Shi ne ya mulki jihar Edo da ke kudancin Najeriya har tsawon shekara takwas daga 1999 zuwa 2007.

EFCC ta gurfanar da shi a gaban wata kotu da ke jihar Enugu a shekarar 2008, inda aka tuhume shi da laifuka 156 da suka danganci cin hanci da rashawa.

An ci gaba da yin shari'ar inda ya sake komawa gaban kotun a shekarun 2011 da 2014 da kuma 2015.

Jolly Nyame

Hukumar EFCC ta gurfanar da tsohon gwamnan Taraba Jolly Nyame a gaban kotu bisa zargin sa da laifuka 41 da suka hada da halatta kudin haram da wawushe kudin gwamantin jihar kimanin naira biliyan 1.64.

A watan Yunin 2016 aka dakatar da shari'ar da zummar har sai ya gabatar da shaidu.

Sai dai kuma a watan Fabrairun 2017 din nan ne ya kasa samun nasarar dakatar da shari'ar, wanda hakan ke nufin EFCC za ta ci gaba da kalubalantarsa a kotu.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Gwamnatin APC ta lashe mulki ne saboda wasu alkawura da suka hada da yaki da cin hanci da rashawa

Ramalan Yero

Hukumar EFCC ta kama tsohon gwamnan jihar Kaduna Ramalan Yero a watan Mayun 2016 kan zarginsa da hannu a karbar wasu daga cikin N23bn da ake zargin tsohuwar ministar mai ta kasar, Diezani Allison-Madueke ta raba wa mutane domin yakin neman zaben tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan.

Ramalan Yero ya zama gwamnan Kaduna ne daga shekarar 2012 zuwa 2015 bayan rasuwar Patrick Yakowa.

GYRA: An gyara wannan sashi sakamakon kuskuren da muka yi tun farko na cewa an gurfanar da Gwamna Lamaran Yaro.

Muna neman afuwa a bisa hakan.

Ibrahim Shehu Shema

Hukumar EFCC ta gurfanar da tsohon gwamnan jihar Katsina Ibrahim Shehu Shema a gaban wata babbar kotun jihar, bisa zarge-zargen cin hanci da rashawa.

Ana dai zargin tsohon gwamnan ne da wasu mutum uku da karkatar da Naira biliyan 11 na kananan hukumomi a lokacin mulkinsa daga shekarar 2007 zuwa 2015.

Daga bisani kotu ta bayar da belinsa, amma ana ci gaba da shari'ar.

Image caption Ana zargin Shehu Shema da yin sama da fadi da wasu makudan kudin Jihar ta Katsina, batun da ya musanta

Chimaroke Nnamani

An tuhumi tsohon gwamnan jihar Enugu da halatta kudin haram a gaban wata babbar kotu da ke Lagos.

EFCC ce ta gurfanar da shi inda ake tuhumar sa da laifuka 105 na halatta kudin haram.

Amma ya musanta zargin. Dama tun a shekarar 2007 aka fara gurafanar da shi amma har zuwa wannan shekara ta 2017 ba a kammala shari'ar ba.

James Ibori

A watan Disambar 2007 ne aka fara tsare tsohon gwamnan jihar Delta James Ibori, bayan ya bayyana a gaban wata kotun birnin London bisa tuhumar sa da aikata laifuffukan da suka hada da halatta dukiyar haram da kuma sama da fadi da zamba cikin aminci.

Shi dai James Ibori tsohon gwamna ne a Jihar Delta mai arzikin mai kuma kusa a jam'iyyar PDP mai mulkin Najeriya a wancan lokaci.

James Ibori dai ya musanta dukkan zarge-zargen da ake yi masa.

Amma ya yi zaman gidan kaso na shekara biyar a London bayan da wata kotu a can ta same shi da laifin halatta kudaden haram. Kuma a yanzu ya koma Najeriya.

Image caption Bala Nigilari zai yi zaman kaso na shekara biyar

James Bala Ngilari

Na baya-bayan nan shi ne tsohon gwamnan Adamawa Mista James Bala Ngilari, inda wata babbar kotu a jihar Adamawan ta yanke wa tsohon gwamnan jihar daurin shekara biyar a gidan kaso saboda sabawa ka'idojin bayar da gwangila.

Alkalin kotun Nathan Musa ya samu tsohon gwamnan da aikata laifuka hudu daga cikin biyar din da aka tuhume shi. Amma ya ce zai daukaka kara.

A Najeriya dai ba kasafai ake yanke wa manyan jami`an gwamnati hukunci ba, kuma ana zargin hakan na da nasaba da jan shari`a har tsawon wani lokaci inda akan shiriritar da maganar.

Labarai masu alaka