Shiga Amurka: Za a raba 'ya'ya da iyayensu a kan iyaka

Mexico Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Amurka za ta raba yara da iyayensu idan suka shiga kasar ba bisa doka ba

Amurka na tunanin raba ya'ya da iyayensu idan aka kama su suna ketare iyakar Amurka da Mexico ba bisa ka'ida ba.

Sakataren tsaron cikin gida John Kelly, ya shaidawa CNN cewa za a yi hakan ne don kokarin hana iyalin da ke tafiya mai hadari daga yankin Amurka ta tsakiya.

An tsare dubban iyaye da yara da ke shiga kasar ta kan iyaka, wadanda da yawan sun tserewa rikici ne a kasashen Honduras da El Salvador.

A yayin yakin neman zabensa shugaba Donald Trump ya mayar da hankali sosai a kan alkawuran harkokin tsaro a iyakar Amurka.

Alkawarin da ya yi na gina katanga a kan iyakar kasar da kudancin Mexico ya karbu tsakanin magoya bayansa.

Rahotannin da suka fito a ranar Juma'ar da ta gabata na nuna cewa wannan sabon kuduri na nufin za a tsare iyaye a lokacin da ake musu shari'a kan bin tsari fitar da su daga kasar.

Trump ya umarci a fara katange Amurka daga Mexico

Amma 'ya'yan nasu za su kasance karkashin kulawar hukumar lafiya da kula da jama'a har zuwa lokacin da za a kai su wajen wani dangi da suke da shi a Amuka ko kuma wasu wakilai da kasar ta amince da su.

A lokacin da ake wa Mista Kelly tamboyoyi a kan rahotannin, ya ce, ''Haka ne, ina la'akari da cewa yin hakan zai hana irin wannan tafiya mai hatsari. Hakan za mu yi tabbas."

Ya kara da cewa, ''Za'a kula da yaran yadda ya kamata yayin da muke kokarin daukar mataki a kan iyayensu.''

Mista Kelly ya kuma ce ya yi duk abin da ya kamata na hana 'yan Amurka ta tsakiya tafiya a yanki cibiya mai hatsari daga Mexico.

Sai dai dan majalisar Democrat daga Texas, Henry Cuellar, wanda yake da wata gunduma mai nisan kilomita 320 daga iyaka kasar, ya soki wannan shawara ta raba iyali.

Inda ya ce, ''Raba iyaye da 'ya'yansu bai dace ba. Irin wannan abu zai jawo a bar batun harkar tsaron iyakar kasar a shiga saba hakkin dan adam.''

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Iyakar Amurka da Mexico

A shekara ta 2014, a lokacin da shugaba Barack Obama ke fadar White House, yawan yara da ake tsarewa wadanda ba sa tare da wani nasu a iyakar kasar ya yi muni sosai, inda aka kama mutum 50,000 a bara.

Wasu sun yi tafiyar ne da iyayensu kuma an kafa cibiya da ake tsare iyalan a can yayin da ake sauraron kakarrakinsu.

Wasu kasashen musulmai ba za su shiga Amurka ba

Amma alkalin wata kotun tarayya a California ya yanke hukunci cewa tsare wadannan yara a wadannan cibiyoyi ya keta doka, ko da kuwa suna take da iyayensu ne, don haka aka bar iyalan suka shiga Amurka.

Tsohon Jami'in hukumar shari'a, Leon Fresco ya ce gwamnatin Mista Obama ta yi tunanin raba 'ya'ya da iyayensu bayan shawarar da kotu ta yanke.

Sa'o'i kadan kafin jawabin Mista Kelly, shugaba Trump ya sanya hannu kan wata doka ta wucin gadi ta hana shigar 'yan gudun hijira da duk baki daga kasashe Musulmi shida, saboda tsoron ta'addanci.

Labarai masu alaka