Indiya: An tsinci 'yan tayin jarirai 19 a kusa da asibiti

Indiya
Image caption Ana samun karuwar zubar da ciki a Indiya

'Yan sanda a yammacin jahar Maharashtra da ke kasar Indiya sun gano 'yan tayin jarirai mata 19 da aka jefar a kusa da wani asibiti.

Babban jami'in 'yan sandan gundumar Sangli ya ce, "An binne 'yan tayin da nufin batar da su."

Dan sandan ya shaida wa BBC cewa sun gano 'yan tayin jariran ne a lokacin da suke binciken mutuwar wata mata sakamakon zubar da ciki da ta yi.

Masu gwagwarmaya sun ce lamarin ya kara tabbatar da cewa har yanzu mata na zubar da ciki duk kuwa da wayar da kan da ake yi musu.

Wani jami'in 'yan sandan yankin mai suna Dattatray Shinde, ya ce matar ta mutu ne sakamakon zubar da ciki, kuma sun ga 'yan tayin jariran a kusa da asibitin lokacin da suka gano gawar matar.

Ya tabbatar da cewa, "Ta mutu ne sanadin zubar da ciki ne .... Mun kama mijin matar kuma yanzu haka muna farautar likitan da ya zubarmata da cikin, wanda tuni ya tsere.

An dai samu faruwar irin wannan lamari a 'yan shekarun baya, inda aka samu jarirai takwas a cikin wata jaka a shekarar 2012, a kusa da tafkin Indore a jahar Madhya Pradesh da ke tsakiyar kasar.

Haka kuma a watan Yunin shekarar 2009 an samu jarirai 15 a magudanar ruwa a gundumar Maharashtras.

Dakta Ganesh Rakh wani mai rajin kare hakkin mata da kananan yara, "Ya ce wannan lamari ya kara tabbatar da cewa har yanzu ana zubar da ciki a kasar."

Ya kara da cewa, "Wannan abin ban tsoro ne, yada zubar da ciki ya zama tamkar kisan gilla a Indiya, wannan ya kara tabbbar da cewa mutane suna daukar yara a matsayin abin wulakantawa."

"Ina tunanin cewa zubar da ciki na faruwa da yawa a Sangli, kuma ina tunanin za mu samu karin masu aikata irin wannan laifi idan aka kama likitan da ke aikata musu hakan," in ji shi.

Zubar da ciki dai babban laifi ne a kasar ta Indiya.

Labarai masu alaka