'Abin da rufe filin jirgin Abuja zai haifar min'

An soki matakin rufe filin jirgin Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Kamfanonin jiragen sama da 'yan kasuwa sun soki matakin rufe filin jirgin

Yayin da a ranar Larabar nan ne ake sa ran rufe filin jirgin saman Abuja, babban birnin Najeriya domin yi masa wasu 'yan gyare-gyare a titin jirgin, masu hulda da filin jirgin sun ce za su fuskanci asara sakamakon rufe filin.

A ranar Litinin ne dai gwamnatin kasar ta sanar da rufe filin jirgin da misalin karfe 12:00 na daren ranar ta Laraba har zuwa makonni shida masu zuwa domin gudanar da gyare-gyaren.

Hakan na nufin matafiya da ke son zuwa ko tashi daga Abuja ta jirgin saman za su rika yin hakan ne a filin jirgin saman Kaduna.

Kaduna dai na da tazarar kilomita 190 daga Abuja, kuma filin jirgin na iya daukar fasinjoji 500 a lokaci guda.

Dangane da yadda matafiya suka ji da wannan sauyin, Naziru Mika'ilu ya tambayi Alhaji Abubakar Mohammad Kangiwa yadda wannan sauyin zai shafi harkokinsa, a inda ya ce zai fuskanci hasara.

Ya kuma ce zai daina amfani da jirgi har sai an kammala gyaran filin jirgin na Abuja.

Ku saurare shi domin jin dalilinsa na daina amfani da jirgin.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Alhaji Abubakar Mohammad Kangiwa