Nigeria: Cutar da ba a san ta ba na kisa a Zamfara

Mazauna kauyen Bindim a jihar Zamfara sun koka da bullar wata cuta da ke kashe mutane Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Mazauna kauyen Bindim a jihar Zamfara sun koka da bullar wata cuta da ke kashe mutane

Gwamnatin jihar Zamfara da ke arewacin Najeriya da hukumar lafiya ta duniya WHO sun tura wata tawagar likitoci zuwa wani kauye da ke jihar domin sanin kowace irin cuta ce ke kisan mutane a can.

Mazauna kauyen mai suna Bindim ne suka kai rahoton bullar cutar.

Wadanda suka kamu da cutar dai kan yi fama da amai da ciwon gabobi musamman kafafu da fizgar jiki da kuma juyewar idanu kafin su rasu.

Mazauna yankin da cutar ta bulla sun ce kawo yanzu mutane kimanin goma sha uku ne cutar ta hallaka a cikin mako daya, a kauyen na Bindim kuma yawancinsu kananan yara ne.

Wasu mazauna yankin dai na fargabar wannan cutar na da alaka da shakar gubar dalma sakamakon ayyukan hakar zinare da ake yi a yankin, ko da yake wata majiyar asibiti ta ce alamun cutar na da kama da na ciwon sankarau.

To sai dai kuma kwamishinan lafiya na jihar, Sulaiman Adamu Gummi, ya ce a yanzu haka ana kan bincike kan wannan cutar domin gano ta.

Kauyen na Bindim dai na cikin yankin karamar hukumar Maru ne, daya daga cikin yankunan kananan hukumomin jihar biyu inda yara sama da 400 suka mutu sakamakon shaka ko hadiyar gubar dalma wadda ta gurbata kauyukansu saboda ayyukan hakar zinare a shekara ta 2010.

Lamarin da hukumomin lafiya na kasa da kasa suka ce shi ne bala'in shakar gubar dalma mafi muni da aka taba samu a duniya.

Labarai masu alaka