Yadda ɓarayi suka yi fashi da shigar 'yan sanda tamkar fim

Armed Police officers guard the plane before the players disembark as the England team arrive at Johannesburg's OR Tambo International Airport for the 2010 FIFA World Cup on June 3, 2010 in Johannesburg, South Africa. Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption An tsaurara tsaro a filin jirgin saman a lokacin gasar kwallon kafa ta duniya wadda aka yi a 2010

Rahotanni daga Afirka ta Kudu sun ce wasu ɓarayi dauke da makamai wadanda suka yi shigar 'yan sanda, sun yi fashi a filin jirgin saman Johannesburg da ke kasar Afirka ta Kudu.

An ce barayin sun shiga wani kebabben wuri kuma suka dauki akwatunan kudi.

Duk da cewar ba a san takamemen yawan kudin da suka sata ba, rahotanni sun ce ta yiwu sun saci miliyoyin daloli ne na kudade kasashen duniya daban-daban.

Kamfanin OR Tambo, da ke lura da filin jiragen saman wanda ya fi ko wanne yawan hada-hada a nahiyar Afirka, ya tabbatar da cewar an yi fashin.

A wata sanarwa da kamfanin da ke kula da filin jirgin ya fitar a kafar yada labarai ta intanet mai suna TimesLive, ya ce, "Ba a yi wani harbi ba, kuma babu wanda ya ji wani ciwo. Kuma 'yan fashin sun gudu."

Amma wata rundunar 'yan sanda ta The Hawks, ta ki fitar da bayanai kan lamarin.

'Tamkar a fina-finan Amurka'

Wani dan jaridar kasar Graeme Hosken, ya shaidawa BBC cewa, "Amma wata majiya daga rundunar 'yan sandan ta bayyana fashin a matsayin wani abu mai kama da shirin fim din Holywood na Amurka."

Dan jaridar ya kara da cewa, barayin, wadanda suka bi ta wata hanyar shiga filin jirgin ta musamman, sun san akwatunan kudin da suke son dauka.

Kafar talabijin din Afirka ta Kudu ta ambato mai magana da yawun 'yan sanda, Athlenda Mathe, tana cewa ba za ta iya tsokaci kan "ko adadin kudin da aka sace ba."

TimeLive ta ce 'yan fashin sun zo ne cikin wata motar da aka rubuta mallakin 'yan sanda a jikinta, kuma suka tsayar da jami'an wani kamfanin tsaro mai zaman kansa wadanda su suke kula da kudaden.

An samu rahotannin satar kayayyaki masu gagarumar daraja a filin jirgin cikin shekarun baya-bayan nan.

Labarai masu alaka

Karin bayani

Labaran BBC