Me ya sa matasa suke rage shaye-shaye?

Young woman smoking
Bayanan hoto,

Duk rukunin mutanen Birtaniya sun rage yawan shaye-shaye amma raguwar ta fi karfi ga rukunin matasa

Hukumar kididdiga ta kasar Birtaniya ta bayar da rahoton cewar duk rukunin mutanen kasar suna rage yawan shaye-shayen da suke yi, amma raguwar ta fi karfi ga rukunin matasa 'yan shekara 18 zuwa 24. Ko me ya sa hakan?

Kadan ne suke fara shaye-shaye

Alkaluman baya-bayan nan na shekarar 2015, na nuna cewa mutum daya cikin mutum biyar 'yan shekara 18 zuwa 24 yana shaye-shaye, watau kenan kashi (20.7 cikin 100).

Amma a shekarar 2010, alkaluman sun nuna cewa mutum daya ne cikin mutum hudu ke shaye-shaye, watau kashi (25 cikin 100).

Sai dai a yanzu kusan kashi 70 cikin 100 na matasa 'yan tsakanin shekar 16 zuwa 24 ba su taba shan sigari ba - kari daga kashi 46 cikin 100 a shekarar 1974 lokacin da aka fara wannan kididdiga.

Haka su ma 'yan shekara 24 zuwa 35 wadanda suka fi yin shaye-shayen sun ragu da kashi 60 cikin 100 - a kari daga kashi 35 cikin 100 a shekarar 1974.

Wata kungiya da ke fafutikar hana shan taba mai suna Action on Smoking and Health (Ash) ta ce "Mun sani cewa matasan da suke shaye-shaye su suke girma su zama manyan mashaya, amma wannan labari na cewa adadi mai yawa na matasa ba su taba shaye-shaye ba, abu ne mai dadi."

An kira Kylie Jenner, wata mai tallan kaya kawa da cewa ba abar koyi ba ce, bayan da ta wallafa hotunanta a shafinta na Istagram lokacin da take shaye-shaye, saboda wannan ba wani abin burgewa ba ne.

Mutane da yawa na barin shaye-shaye

Sabuwar kididdigar ta nuna cewa kashi 23.3 cikin 100 na matasa 'yan tsakanin shekara 16 zuwa 24 sun daina shaye-shaye a shekarar 2015, idan aka kwatanta da kashi 21.4 cikin 100 a 2010, da kuma kashi 13.4 a shekarar 1974.

Kungiyar ta Ash ta ce "Wannan ci gaba ya samu ne sakamakon hadin gwiwar dokoki da manufofin gwamnati masu amfani tare kuma da hadin kai tsakanin matasan a shekarun da suka gabata, wanda kuma ya taimaka sosai wajen fahimtar matasan ta barin shaye-shayen."

Daraktan tsare-tsare Hazel Cheeseman ya ce "Samun al'umar da kadan ne daga cikin matasanta ke shaye-shaye, sannan kuma da yawa daga mashayan na barin shaye-shaye, zai taimaka wajen kare lafiyar al'mma masu tasowa, da kuma rage mutuwar daruruwa da kuma dubban mutane."

Ya kara da cewa "Dole gwamnati ta gaggauta samar da sabon tsari a kan shaye-shaye ga 'yan kasar, sannan kuma ta tabbata ta dauki nauyin tsarin."

Fitowar shan sigari ta na'urar lantarki

Sabon rahoton ya nuna cewa a shekarar 2015 mutum uku cikin mutum 100 'yan tsakanin shekara 16 zuwa 24 na amfani da na'urar shan sigari ta lantarki, wanda ya karu daga mutum daya cikin 100 a shekarar 2014.

A gaba dayan jumulla mutum miliyan 2.3 a Burtaniya na amfani da su.

Sai dai wasu na ganin cewa amfani da na'urar lantarki wajen shan sigari zai kara jefa matasan cikin harkar shaye-shayen.

Sannan kuma masu sukar lamarin na cewa dandadon kayan marmarin da na'urar ke da shi yana jan hankalin yara.

A watan Disambar 2016 babban likitan tiyata na Amurka ya ce amfani da na'urar shan sigari ga kananan yara "babban al'amarin lafiya ne da ya shafi al'umma."

Sai dai kungiyar Ash ta ce alkaluman baya-bayan nan "sun tabbatar da cewa mafiya yawan masu amfani da ita tsofaffin mashaya ne."

Ta kara da cewa "alkaluman sun nuna cewa mafiya yawan masu amfani da ita suna neman yadda za su inganta lafiyarsu, saboda babban dalilinsu na amfani da ita shi ne saboda kare lafiyarsu."

Mashayan na komawa amfani da na'urar ne saboda suna tsammanin cewa tana rage sinadarai masu cutarwa, wadanda ke haddasa cutar daji da sauran cututtukan da ke da alaka da shaye-shaye.