Me ya sa dalibai ke faduwa jarrabawar Ingilishi?

Dalibai a Najeriya Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Dubban dalibai ke faduwa jarrabawar Ingilishi da Lissafi a Najeriya

A kalla kashi 80 cikin 100 na dalibai a Ingila da ba su yi nasarar cin jarabawar su ta GCSE da makin C a darussan lissafi da kuma Inglishi ba ne ke sake zaunawa jarabawar.

Yanzu haka dai akwai dubun-dubatar dalibai a kasar da suka kasa ci gaba da karatu sakamakon kasa samun nasara a darusan na lissafi da kuma Ingilishi.

A Najeriya ma dai, kanwar ja ce in ana maganar faduwa jarabawar darussan lissafi da Ingilishi a makaranatun sakandire.

Kuma a duk shekara dubban dalibai ne kan yi tuntube da wannan matsala, wadda kan hana su damar shiga jami'o'i da sauran makarantun gaba da sakandire.

Matsalar dai a iya cewa tamkar ruwan dare ne a kasar, sakamakon haka ne ma, har makarantu na musamman masu zaman kansu kan bude a sassa daban-daban na kasar, don yi wa dalibai bitar da za ta kai su ga cin nasarar jarabawar.

Wakilin BBC AbdusSalam Ibrahim Ahmad ya ziyarci daya daga cikin wadannan makarantu, mai suna Ivory Science Academy da ke nan birnin Enugu, a Kudancin kasar, inda dubban dalibai ke shirin yin

jarrabawa a watan Afrilu.

Cynthia Offor, 'yar shekara goma sha bakwai, dalibar wannan makaranta ce, ta kuma bayyana yadda matsalar faduwa jarabawar darasin lissafi ta tarnake ci gaban karatunta.

Ta ce, Sakamakon darussan da na yi jarabawa kan su duk sun yi kyau matuka, sai dai ban sami shiga jami'a ba, saboda na fadi jarabawar darasin lissafi, shi ya sa dole sai na sake maimaita jarabawarsa."

"A gaskiya na yi bakin ciki da wannan al'amari, amma dai ina fata in sami nasarar lashe wa a wannan karon," in ji ta.

Jeniffer Chioma Ude, wata dalibar, ita ma ta shaida wa BBC cewa, tana cike da fatan samun nasarar jarabawar, shi ya sa ma ta shiga wannan makaranta ta musamman.

''Ina so in sami nasarar jarabawata ta WAEC a tashin farko, ba tare da na maimaita ta ba, musamman ma dai darusan Turancin Ingilishi da lissafi. Ina da kwarin gwiwa kan haka,'' in ji Jennifer.

Shi kuwa Emeka Osogu, wani dalibin mai shekara 16, zai yi jarabawar kammala sakandiren ce a karon farko. Kuma ya ce yana fatan samun nasara a bugu daya.

Ya kara da cewa, ''Saboda yawan kudin da akan biya don yin wannan jarabawa yana da yawa matuka, kuma abin ya iya gagarar iyaye su kara biya wa mutum nan, don ya maimaita jarabawar nan gaba.''

Hakkin mallakar hoto Getty Images

'Da sauran rina'

Dokta Nwokoro Albert, masani ne a fannin ilimi, kuma wakilin BBC ya tambaye shi ko me ya sa dalibai ke yawan faduwa jarabawar darusan na lissafi da Ingilishi?

Dokta Nwokoro ya ce, ''Idan ana da iyayen da ba su damu da gina al'adar karance-karancen littattafai a gidajensu ba, ina makomar wadannan yara da ke tasowa?"

"Sannan su ma yaran a nasu bangaren, suna fama da abubuwa da dama da ke dauke masu hankala a zamanin yau, kamar kafofin sadarwa na intanet, da wayar salula da kwamfuta da dai sauransu," in ji shi.

Ya kara da cewa, "Akwai kuma matsalar karancin kwararrun malamai da kayan aiki, da kuma duk wani abu da zai karfafa harkar koyarwa yadda ta kamata.''

Masanin na fannin ilimi, yana gani ya zama wajibi dukkan wandanda abin ya shafa su tashi tsaye wajen shawo kan matsalar.

Labarai masu alaka