Nigeria: An sanya dokar hana fita a Ile Ife

Ibrahim Idris, Sifeto Janar na 'yan sanda Hakkin mallakar hoto Facebook
Image caption An sanya dokar hana fitar har zuwa juma'a

Gwamnatin jihar Osun da ke kudu maso yammacin Najeriya, ta kafa dokar hana fita a birnin Ile-ife bayan wani rikici mai alaka da kabilanci da ya barke ranar laraba.

Dokar dai wadda aka sanya ta tsawon kwana uku tana farawa daga karfe shidan safe zuwa bakwai na yamma.

Rahotanni sun ce mutane da dama sun rasa rayukansu sannan wasu kuma sun jikkata sakamakon rikicin tsakanin Hausawa da Yarbawa.

An dai ce al'amarin ya samo asali ne bayan da wata mai sayar da abinci Bayarbiya ta mari wani Bahaushe sakamakon sa-in-sa, a inda shi kuma ya rama marin.

Bayan nan ne kuma sai matar ta shaida wa mijinta wanda shugaba ne na 'yan tasha abin da ya faru, a inda ya gayyaci abokansa suka farwa mutumin.

Mataimakin kwamishinan 'yan sandan jihar, Aminu Koji ya shaida wa BBC cewa: "al'amarin ya rincabe ne da safiyar ranar Laraba bayan 'yan tashar sun kara far wa mutumin da ya rama mari."

Hakan ne kuma ya sa rikicin ya bazu har ya janyo asarar rayuka da dukiya.

Mista Koji ya kuma ce tuni kura ta lafa kuma suna bincike kan musabbabin al'amarin.

Sannan kuma jami'an tsaron sun kwashe wasu mutane zuwa hedikwatar 'yan sandan jihar domin ba su mafaka.

Kusan za a iya cewa wannan ne karon farko da rikicin kabilanci ke faruwa tsakanin Hausawa da Yarbawa a birnin na Ile Ife mai tsohon tarihi.