Guatemala: Gobara ta kashe yara a gidan marayu

An garzaya da wadanda gobarar ta rutsa da su zuwa asibiti Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An garzaya da wadanda gobarar ta rutsa da su zuwa asibiti

Wata gobara da ta tashi a wani gidan marayu da ke Guatemala ta kashe akalla matasa 'yan mata goma sha tara, yayin da wasu da dama kuma suka samu raunuka.

Har yanzu ba a kai ga gano musabbabin tashin gobarar ba, amma rahotanni na cewa ba mamaki da gangan aka haddasa gobarar.

A ranar Talatar da ta gabata sai da 'yan sanda suka shiga tsakani bayan wata zanga-zanga ta barke a gidan, inda yara kusan 60 suka tsere .

Wasu daga cikin yaran dai na korafin ana gallaza musu, har ma da cin zarafinsu ta hanyar lalata da su.

Gidan marayun dai ya na ba wa sama da yara 500 mafaka, wanda yawancin su, tashe-tashen hankula ya raba da muhallansu, duk da cewa a ka'ida kamata ya yi a ajiye yara 400 a cikin gidan.

Labarai masu alaka