'Ba guba ce ke kisa a Zamfara ba'

Gwamnatin Zamfara ta ce an shawo kan cutar da ta bulla a Bindim Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Gwamnatin Zamfara ta ce an shawo kan cutar da ta bulla a Bindim

Gwamnatin Jihar Zamfara a Najeriya ta ce an yi nasarar shawo kan cutar da ta bulla a kauyen Bindim da ke jihar wadda ta hallaka mutane da dama.

Mazauna kauyen sun ce mutane 15 ne suka mutu a makon daya gabata bayan da suka kamu da cutar.

Kwamishinan lafiya na jihar, Alhaji Sulaiman Adamu Gummi ya shaidawa BBC cewa tawagar likitocin da aka tura kauyen ta ce yau lamarin da sauki a kan kwanakin da suka shude.

Kwamishinan ya ce ana kyautata tsammanin cutar sankarau ce ta bulla a kauyen saboda sauyin yanayin da aka shiga na zafi.

Alhaji Suleiman, ya cigaba da cewa yanzu haka an dauki samfurin jinin wadanda suka kamu da cutar an tura Abuja da Sokoto domin a gano ainihin wacce irin cuta ce.

Kwamishinan ya jaddada cewa wannan cuta da ta bulla kauyen Bindim ba gubar dalma ba ce kamar yadda wasu ke fada.

Alamomin cutar dai sun hada da amai da ciwon gabobi musamman kafafu da fizgar jiki da kuma rikidewar idanu.

Labarai masu alaka