Shaye-shaye na kamari a Nijar

Gwamnatin Nijar ta ce dole a hada hannu da karfe wajen magance matsalar shaye-shaye a kasar
Image caption Gwamnatin Nijar ta ce dole a hada hannu da karfe wajen magance matsalar shaye-shaye a kasar

Jami'an tsaro a Jamhuriyar Nijar sun zakulo tabar wiwi mai nauyin kilogram 80 daga wani gida a birnin Damagaram a cikin wani samame da suka kaddamar kan maboyar masu safarar miyagun kwayoyi a garin.

Tuni dai da garuruwa daban-daban na kasar suka zama wurin yada zango ga masu safarar bil'adama da kuma masu fataucin miyagun kwayoyi tsakanin kasashen yammacin Afrika da Turai.

Gwamnan jihar Damagaram Isa Musa ya ce an gudanar da samamanne saboda a kama wadanda suke sha da ma sayar da kayan shaye-shaye masu illa, da kuma tabbatar da zaman lafiya a jihar.

Gwamnan ya ce masu sayar da ire-iren wadannan kayayyakin shaye-shayen matasa ne 'yan jihar, wadanda ba abin da suka sa gaba sai su samu kudi ta kowacce hanya.

Daga nan, gwamnan ya yi kira ga al'ummar jihar da ma sauran 'yan kasar baki daya da su ba wa jami'an tsaro hadin kai a yunkurin da ake na ganin an kawar da shaye-shaye a tsakanin matasa.

Kazalika su ma matasan ya kamata su yi karatun ta nutsu su dai na wannan dabi'a, su nemi abin yi domin dogaro da kansu inji gwamnan.

Labarai masu alaka