Nigeria: An sa tsaro sosai a hanyar Abuja-Kaduna

Abuja airport
Image caption Lalacewar titin ya janyo giyar wani jirgin Afirka ta Kudu ta lalace a kwanakin baya

Rahotanni na cewa gwamnatin Najeriya ta kara saka matukar tsaro a kan titin da ke tsakanin babban birnin kasar Abuja, zuwa garin Kaduna.

Wannan na zuwa ne bayan da aka rufe filin jiragen saman Abuja na wucin-gadi domin a gyara shi, inda aka karkatar akalar jiragen da ke sauko zuwa Kaduna.

Hakan na nufin a yanzu sai dai fasinjojin da ke bin jirgin sama su dinga tafiya tsakanin biranen biyu a mota, a kan hanyar da ta yi kaurin suna wajen sace mutane.

Rahotanni sun ce an girke jibga-jibgan motocin 'yan sanda a duk tsakanin nisan kilomita biyu a kan hanyar.

Gwamnati ta bayar da umarnin rufe filin jiragen saman ne saboda gyaran titin da jiragen ke sauka wanda ya lalace.

Mafi yawan kamfanonin jiragen kasashen waje sun ce ba za su dinga sauka a Kadunan ba saboda matsalar tsaro.

Amma kamfanin jirage na Ethiopia ya amince da sauka a Kadunan, hakan tasa ya dinga samun yabo daga wajen mutane a shafin Twitter.

Tuni dai hukumar kula da sufurin jiragen sama ta Najeriya ta ce an gudanar da shirye-shirye wajen daukar matakan kare lafiyar fasinjoji.

Ta ce matakan da suka dauka sun hada da amfani da bas-bas da kuma 'yan sanda.

Hukumar ta kara shaida wa kamfanin dillanci labarai na Reuters cewa an aika 'yan sanda zuwa yankin, domin tabbatar da harkokin tsaro sannan kuma an gyara hanyoyin mota.

Titin da jiragen ke sauka dai ya fara bukatar gyara ne tun a shekarar 2002, shekara 15 da ta gabata, amma an zargi gwamanatocin da suka gabata da rashin mayar da hankali kan hakan.

Masu sharhi na danganta hakan da matsalar cin hanci da ta yi kamari a kasar.

Amma a yanzu manyan ramukan da ke kan titin saukar jiragen na da matukar hadarin da ka iya jawo faruwar wani abu marar kyau, don haka ba zai yiwu a ki mayar da hankali wajen gyara shi ba.

Tun a shekarar 1982 aka gina titin, kuma a ka'ida zai iya tasirin aikin shekara 20 ne kawai.

Birnin Kaduna dai na da tazarar kilomita 190 daga Abuja, babban birnin kasar.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Ra'ayoyin 'yan Najeriya

'Yan Najeriya da dama dai sun fara bayyana ra'ayoyinsu a shafukan sada zumunta da muhawara kan yadda suke kallon wannan lamari na tsauraro tsaro a hanyar Abuja zuwa Kaduna a wannan lokaci.

Wasu na ganin don dai lamarin ya hada da zirga-zirgar masu ido da kwalli ne shi ya sa aka girke jami'an tsaro sosai a hanyar da ya kamata a ce ko yaushe ne aka mata irin wannan 'gatan'.

Barrister Sunusi Musa ya rubuta a shafinsa na Facebook cewa; "Wato ni dai ina rokon Allah ya yi min katangar karfe da talauci. Wato shi talaka na fuskanci ba wani abu da ake yi don shi, sai dai a yaudare shi. Kana gani tuntuni na hakura da bin hanyar Kano zuwa Abuja idan magariba ta yi saboda tsoron barayi da rashin kyawun hanya. Amma mallam ka ga yanzu saboda masu abin za su rinka bin hanya, an gyarata sannan duk kilomita biyu an saka jami'an tsaro."

Image caption Yadda fillin jirgin sama Kaduna ya kasance a yau

A shafin Twitter ma Ibrahim Salihu ne ya rubuta cewa, "A kalla mu ma za mu mori dadin titin da kuma tsaro sosai na tsawon mako shida."

Shi ma Hamisu Nasidi Baban Auwaab ya rubuta: "Ranar Lahadi na bar Kaduna wajen karfe 8 na dare zuwa Abuja, Ni kadai na yi tsaki na ce, kai Nigeria mun shiga uku, ashe babu wani abu da ba za'a iya yin sa ba a kasar nan? Kawai zalunci ne da mugunta ya hana? Don Allah ji hanyar nan sai inda kaga dama zaka bi, ba wani tunanin rami."

Image caption Yanayin filin jrigin saman Kaduna

To ita ma dai hukumar kula da kare afkuwar hadurra ta Najeriya FRSC, ta ce ta girke jami'ai fiye da 20 da kuma motocin sintiri 15 da za su dinga aiki na sa'o'i 24 a kan titin Abuja zuwa Kaduna don kare afkuwar wani mummunan abu.

Labarai masu alaka