BH: Australia za ta ciyar da yara 12,000 a Nigeria

UN Hakkin mallakar hoto AP
Image caption A watannin baya ne Majalisar Dinkin Duniya ta ce yara 400,000 na bukatar tallafin gaggawa domin kubutar da su daga yunwa

Kasar Australiya ta ce za ta ciyar da yara 12,000 nan da shekara hudu a arewa maso gabashin Najeriya, wadanda rikicin Boko Haram da ya raba su da gidajensu.

Jakadan kasar Australiya a Najeriya, Paul Lehman, wanda ya bayar da sanarwar, ya ce za a yi amfani da shirin ciyar da yaran domin ceto su daga tsananin yunwa da suka shiga.

Yunkirin ciyar da yara 12,000 da ofishin jakadancin Australiya a Najeriyar zai yi ya zo ne watanni kadan bayan Majlisar Dinkin Duniya ta ce yara 75,000 ka iya mutuwa saboda yunwar da ake fama da ita a yankin arewa maso gabashin Najeriya.

Mista Lehman ya ce shirin ciyarwar wanda zai ciyar da yara 500 a ko wane wata, wani gwajin ne wanda zai nuna yadda za a dauki matakai mafi inganci wajen ceto rayuka a yankin.

An ya adadin yaran da ake son ciyarwa bai yi kadan ba idan aka yi la'akari da yawan mutanen da ke cikin tsananin bukatar abinci a arewa maso yammacin Najeriya?

Hakkin mallakar hoto .
Image caption .

Tambayar da wakilinmu ya yi wa jakadan Australiyan a Najeriya kenan, inda shi kuma ya ce, "Hakika, gaskiya ne. Amma ba ma da'awar cewa za mu warware dukkan matsalolin ta wannan shirin. Abin da muke son yi shi ne mu nuna abin da za a iya yi, da kuma hanyar yin hakan."

Kungiyar bayar da agaji ta Empower54 wadda za ta hada hannu da ofishin jakadancin Australiya a Najeriya a shirin, ta ce za a hada abincin da za a ciyar da yaran ne a jihohin da ke makwataka da wuraren da matsalar yunwar ta fi kamari.

Shugabar kungiyar, Modupe Ozolua, ta ce sun fara tattaunawa da jihohin za su karbi bakuncin wurin hada abincin wanda ta ce zai kai irin yadda Majalisar Dinkin Duniya take bukata.

"Za ka iya ce wa abinci mai gina jiki da aka yi da gyada ne, amma ba shi ba ne saboda wannan yana da sinadarai masu yawa. Akwai gyada da wata rin madara da suga da wani irin mai da kuma wasu sinadaran bitamin da za a saka ciki. Saboda haka abincin ya kunshi ababen ban sha'awa, amma ingantacce ne saboda sai an auna komi."

Daya daga cikin bukatun 'yan gudun hijirar da ke arewa maso gabashin Najeriyar dai ita ce a kara kaimi wajen taimaka musu domin kawar da barazanar da yunwa take wa rayuwarsu.

Labarai masu alaka