Wenger: Ra'ayin magoya bayan Arsenal zai yi tasiri kan makomata

Arsene Wenger

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Wasu masu magoya bayan Arsenal na son Arsene Wenger ya bar kungiyar

Kociyan Arsernal, Arsene Wenger, ya ce ra'ayin masu goyon bayan kungiyar zai yi tasiri kan ko zai ci gaba da jan ragamar kungiyar badi ko kuma a'a.

Wasu tarin magoya bayan Arsenal ne suka yi zanga-zanga bayan lallasa kungiyar da Bayern Munich ta yi 5-1 a gasar Zakarun Turai.

"Ba zai zama dalili mafi muhimmanci ba, amma za ka yi la'akari da shi mana,"in ji Wenger.

Ya ce: "Na yi aiki tukuru na shekara 20 domin farin cikin masu sha'awarmu, kuma idan ka sha kaye, ba za su ji dadi ba".

A wata sanarwar da aka wallafa a shafin intanet na kungiyar, shugaban Arsenal, Sir Chips Keswick ya ambato irin wadannan ra'ayoyin, amma bai fito da matsaya kan makomar Wenger ba.

Ya ce: "Muna sane da yadda aka mayar da hankali kan kulab din da kuma muhawarar da ake yi."

"Muna girmama cewar masu sha'awarmu ta 'yanci ra'ayoyinsu, amma za mu ci gaba da jan ragamar wannan babbar kungiyar bisa la'akari da bukatarta ta din-din-din.

"Wenger yana da kwantiragin da zai kai karshen kakar nan. Duk wata shawara da za mu yanke, zamu yanka tare da shi ne, kuma za mu bayyana hakan lokacin da ya dace," in ji shi.

Ana tsammani Wenger, wanda yake jan ragamar Arsenal din tun watan Oktobar 1996, zai bayyana ko zai tsaya a kungiyar a kakar badi, amma ya musanta cewar shi ya riga ya shaida wa 'yan wasan Arsenal abin da zai yi.