Iraki: Yan kunar bakin wake sun kashe mutum 26 a gidan biki

Map showing Hajaj and Tikrit in Iraq

Wasu 'yan kunar bakin-wake biyu sun tayar da bam a wani gidan biki a kauyen Tikrit da ke arewacin birnin Baghdad, inda suka hallaka kansu tare da wasu mutum 26 din.

Kungiyar IS ta ce biyu daga cikin mayakanta ne suka kai harin a ranar Laraba.

Jami'ai sun bayyana cewa, dan kunar bakin-waken na farko ya shiga cikin wasu maza da ke rawa inda ya tayar da bam din da ke jikinsa, yayin da na biyun ya tayar da nasa a lokacin da mutane suka taru don taimakawa a wajen da na farkon ya tashi.

Mai magana da yawun Karamar Hukumar garin ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AP cewa, mafiya yawan wadanda suka mutu a gurin yara ne.

Kungiyar IS ta ce ta shirya kai harin ne wajen taruwar sojojin hadaka wadanda mafi yawansu 'yan shi'a ne da kasar Iran ke goya musu baya.

Kungiyar IS ta bayyana a wani shafinta na sada zumunta, cewa maharan sun gwabza da dakarun hadakan kafin tayar da bam din.

A kalla wasu mutum 25 din sun jikkata.

Nausawa birnin Mosul

Kamfanin AP ya ce, taron bikin, wanda aka yi a yammacin ranar Laraba, na wasu mutane ne 'yan gudun hijira daga birnin Anbar da ke yammacin Iraki, inda mafi yawan mutanen yankin ke adawa da IS.

Masu tayar da kayar bayan sun kwace yankin Arewaci da tsakiyar Iraki, wadanda suka hada da Tikrit a lokacin bazarar shekarar 2014, ammam a watan Afrilun shekarar 2015 ne sojojin Iraki suka fatattake su daga birnin.

Sai dai sun ci gaba da kai hare-hare cikin birni da kewayensa, inda nan ne ainiihin garin tsohon shugaban kasar Iraki, Saddam Hussein.

Al'amarin na zuwa ne a yayin da dakarun gwamnatin Iraki suke kokarin kwace iko da birnin Mosul daga hannun kungiyar IS.

Bayan da suka sami nasarar iko da gabashin birnin a watan Janairu, a yanzu sojojin na kara nausawa yammacin birnin inda yake da cunkosan jama'a.

This week they have taken a government complex and the Badoush prison, where IS are alleged to have killed 600 mainly Shia inmates.

A wannan makon ma sun sake kwace iko da wani ginin gwamnati da kuma gidan yarin Badoush, inda aka yi zargin kungiyar IS ta kashe 'yan shi'a kusan 600.

Labarai masu alaka