'Na yi ɓarin ciki sau biyar saboda magagin baccin mijina'

Andrew tare da yaranta guda uku Hakkin mallakar hoto Roberts family
Image caption Andrew Roberts tare da 'ya'yansa

Lindsey Roberts wacce bazawara ce a yanzu, ta ce sau biyar tana barin ciki saboda dukan da mijinta Andrew yake yi mata a lokacin da yake cikin magagin bacci a yayin da a yanzu ta gurfanar da hukumar tsaron kasar a gaban kotu.

Ta shaida wa BBC cewa "ban san mijin nawa yana da magagin bacci ba, sai lokacin da nake da juna biyu".

"A lokacin ina da cikin sati biyar, kuma da haka ne na yi barinsa".

Lindesy, 'yar asalin garin Bicester, ta ce ta yi barin cikin har sau biyar, sakamakon dukanta da mijinta, Andrew roberts yake yi a lokacin magagin baccinsa.

Kofur Roberts ya shiga aikin soji ne tun yana dan shekara 17, sannan kuma ya shiga tawagogin yaki har sau tara, wadanda suka hada da guda biyu a Iraki, da kuma uku a Afghanistan.

Hakan dai ya janyo masa cutar magagin bacci, har ya yi kokarin kashe kansa.

Ya mutu ne sakamakon harin igwa da kungiyar Taliban ta kai musu ranar hudu ga watan Mayun shekarar 2012.

Ya samu ganin 'ya'yansa kafin ya ya rasu.

"Mun samu ganin ma'auratan tare da 'ya'yansu , sannan kuma yana kiransu a waya a kowacce rana".

Lindesy tana tuna shi tare da alhinin cewa "mijina kyakkyawan ne, zai iya yi wa kowa komai, yana da kula, mutum ne na mutane".

Hakkin mallakar hoto Roberts family
Image caption Andrew ya shiga tawagogin yaki tara daga Birtaniya

Lindesy ta bayyana cewar ta yi barin nata ne a cikin shekaru masu yawa.

A cewarta "Ba koyaushe lalurar tasa ke tashi ba, saboda haka ba mu daina kwana gado daya da shi ba, saboda ba za a iya hasashen yaushe abin zai faru ba".

Ta kara da cewa tana yin barin ne a cikin kwanaki ko makonnin da ya doke ta.

Lindesy ta ce duk jikinta yakan kurmance, duk da cewa suna kwanciya tare, idan ta tuna yadda suka faro.

"Ba na so na sa shi cikin damuwa. Sai kawai na sauka daga kan gado idan na ji abin ya fara tashi", in ji ta.

Liundsey ta ce Andrew ya doke ta, cikin magagin bacci har sau uku a cikin mako guda, lokacin da ya dawo daga yakin Afghanistan karo na biyu a shekarar 2009.

'Sojoji suna sane'

Sau takwas Lindsey tana samun ciki da Andrew, kuma suna da 'ya'ya uku wadanda shekarunsu suka kama daga takwas, da goma zuwa 11.

Ta ce duk yaran kanana ne lokacin da wannan lamari ke faruwa "amma yanzu sun san abin da ya faru da mahaifinsu".

"Amma kuma suna iya tuna kadan daga cikin abubuwan da suka faru", in ji ta.

Hakkin mallakar hoto Roberts family
Image caption Andrew da Lindsey ranar daurin aurensu

A shekarar 2009 ne lamarin Andrew ya yi kamari, sai zaman ma'auratan ya faskara, amma duk da haka ba su rabu ba.

Ta ce daga baya ne sojoji suka gano halin da yake ciki na magagin bacci, wanda kuma yake da illa ga lafiyarsa.

Lindsey ta kara da cewa "A shekaru biyu da suka wuce, lokacin yana raye, sojojin sun san halin da lafiyarsa ke ciki".

Sun ziyarci ma'auratan, yayin da yake yunkurin kashe kansa kuma sojojin sun san cewa ba a cikin hayyacinsa yake ba.

Lindsey ta ce "Andrew zai iya rayuwa idan da ya samu kulawa ta musamman".

Shekara daya kafin ya tafi yakinsa na karshe, ya samu gagarumar rashin lafiya da ta shafi kwakwalwa. Hakan ya sanya dole aka fasa tura shi zuwa yakin.

Ta ce "Ya yi ta yunkurin kashe kansa a fili har abin ya kai matuka".'Mata suna shan wahala'

A yanzu dai Lindesy ta gurfanar da hukumar tsaron kasar a gaban kuliya, a kan laifuka guda biyu. Laifi na farko shi ne rashin kulawa da hukumar ta nuna a kan mijin nata na rashin barinsa ya koma Afghanistan a shekarar 2012. Sai kuma raunukan da ita kanta ta ji sakamakon dukan da mijinta ya yi mata cikin magagin baccinsa.

Lindsey na fatan wannan zai sa a gudanar da bincike, ko kuma cikakken binciken da ya shafi al'umma, wanda kuma zai inganta matakan kare sojoji nan gaba.

Ta kara da cewa "dalilin da ya sa muka shigar da kara shi ne, don hukuma ta san cewa mata su ne na biyu a wadanda abin ya shafa. Amma babu wanda ya san wannan".

Mai magana da yawun hukumar tsaron kasar ya ce "ba za mu ce komai ba a kan wannan batu ba, amma lafiyar kwakwalwar kowanne mutum da yake yi wa kasa aiki na da matukar muhimmanci, shi ya sanya ma muke kira ga duk wanda ba shi da lafiya da ya zo domin samun taimakon da ya dace lokacin da aka kai shi, ko bayan an kai shi filin daga".

Hakkin mallakar hoto Roberts family
Image caption Andrew tare da 'ya'yansa biyu

Labarai masu alaka

Karin bayani