Nigeria: INEC ta fitar da jadawalin zaben 2019

Hakkin mallakar hoto CHANNELS TV
Image caption INEC na so ta rika yin zabe a lokaci guda

Hukumar zaben Najeriya, INEC ta fitar da jadawalin zaben kasar na shekarar 2019.

Wata sanarwa da kakakin hukumar Nick Dazang ya aike wa BBC ta ce za a gudanar da zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar dokokin tarayya ranar Asabar, 16 ga watan Fabrairu.

A cewar Mr Dazang, za a yi zaben gwamnoni da na 'yan majalisun jihohi da kuma na birnin tarayya ranar biyu ga watan Maris.

Kakakin hukumar zaben ya ce daga yanzu za a rika gudanar da zabukan ne a ranakun da aka ambata ba tare da an dage ko jinkira gudanar da su ba.

Ya ce INEC ta gudanar da taro na masu ruwa da tsaki a watan Janairu, inda ta jaddada bukatar yin shirye-shirye da wuri na gudanar da manyan zabukan ba sai lokaci ya kure ba.

A shekarar 2019 ne dai INEC za ta gudanar da zabuka a karon farko a karkashin jagorancin Farfesa Mahmood Yakubu.

Ya karbi jagorancin hukumar ne bayan saukar Farfesa Attahiru Jega, wanda ya gudanar da babban zaben kasar na shekarar 2015, wanda Shugaba Muhammadu Buhari ya lashe.

Labarai masu alaka