Shugaba Buhari zai koma Nigeria bayan hutun jinya

President Muhammadu Buhari Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Jinyar shugaba Muhammadu Buhari da ƙara hutun da ya yi ta janyo ce-ce-ku-ce a tsakanin 'yan Nijeriya

Fadar shugaban Nijeriya ta ce a ranar Juma'a ce ake sa ran shugaban ƙasar Muhamadu Buhari zai koma gida bayan jinyar da ya yi a ƙasar Burtaniya.

Tun a ranar Talata 19 ga watan Janairu ne shugaba Buhari ya tafi hutu da kuma ganin likita.

Daga bisani ya tsawaita hutun nasa, bisa abin da fadarsa ta ce, umurni ne na likitansa, domin yi masa gwaje gwaje da kuma kara hutawa.

Wata sanarwa da mai ba shi shawara kan harkokin yada labarai, Femi Adeshina ya fitar ta ce Muhammadu Buhari ya gode wa ɗaukacin al'ummar Nijeriya da ma na kasashen waje kan addu'o'in da suka rika yi masa na fatan alkhairi.

Hutun jinyar da kuma tsawaita shi da shugaban ya yi, sun janyo muhawara sosai a tsakanin 'yan Nijeriya.

A baya-bayan nan wayar da ya yi da gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, lokacin da aka fara jin muryarsa tun bayan zuwa hutun jinyar, ya sa zuciyar 'yan ƙasar da dama kwanciya.

An yi ta ganin hotunan Muhammadu Buhari da wasu fitattun 'yan Nijeriya yayin ziyarar da suka riƙa kai masa lokacin da yake jinya a London.