Budurwa ta kashe saurayinta da ruwan bilici

Yasmine Elder
Bayanan hoto,

'Yan sanda sun kama Yasmine Elder da maryacen ranar Litinin

An tuhumi wata matashiya mai shekara 24 'yar asalin Chicago a Amurka da aikata kisan kai bayan ta maƙure saurayinta ta kwankwaɗa masa ruwan bilici a lokacin da suke fada.

Ana zargin Yasmine Elder da tumurmusa Darrius Ellis, mai shekara 26 a ƙasa, kafin ta kwankwaɗa masa ruwan bilici ya wuce ta maƙogwaronsa.

Masu bincike sun ce lamarin ya faru ne a ranar Litinin lokacin da saurayin da budurwar suke musu a cikin wata mota da suka ajiye a gefen hanya.

Bayan sa'o'i ne 'yan sanda suka samu Darrius Ellis yashe a kan titi.

Likitoci sun ce matashin ya mutu a asibiti inda aka garzaya da shi sakamakon abin da suka kira "ɗirka masa wani sinadari da ka iya ƙona kayan ciki".

Dangin mamacin sun faɗa wa Chicago Tribune cewa yana da ɗa mai shekara biyar.