Dubban 'yan gudun hijira na koma wa gida Nigeria

Boko Haram refugees Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Kananan yara maza da mata na daga cikin 'yan gudun hijirar da suka fi shan wahala a rikicin Boko Haram

Hukumar ba da agajin gaggawa ta Nijeriya ta ce 'yan gudun hijira fiye da dubu ashirin da biyu wadanda rikicin Boko Haram ya raba da muhallansu ne suka kwarara cikin kasar a baya-bayan nan.

Hukumar ta ce jami'anta da takwarorinsu na jihar Borno da kuma jami'an kula da shigi da fice sun yi rijistar mutum dubu 22 da 463 da suka shiga Damask daga jamhuriyar Nijar.

Babban jami'in hukumar a shiyyar arewa maso gabashin Nijeriya, Muhammad Kanar ya ce matakin ya biyo bayan yarjejeniyar da aka cim ma tsakanin Nijeriya da kasashen Nijar da Kamaru a kan komawar 'yan gudun hijirar zuwa gida.

Ya ce garuruwan kan iyaka irinsu Damasak da Gamboru da Banki za su ci gaba da ganin kwararar 'yan gudun hijirar daga ƙasashe maƙwabta.

Image caption A baya-bayan nan an samu lafawar hare-haren da Boko Haram ke kai a yankin arewa maso gabashin Nijeriya

A cewarsa ya zuwa yanzu sun tantance sama da mutum dubu 22 a Damasak waɗanda suka tsugunnar da su kafin a gyara muhallansu don su koma ciki.

Jami'in ya ce yanzu suna shirya batun ciyar da 'yan gudun hijirar, haka kuma akwai manyan ƙungiyoyin ba da agaji na duniya da za su kai ziyara a ƙarshen wannan mako don tantance buƙatun mutanen.

Muhammad Kanar ya ce jami'an kula da shige da ficen Nijeriya da kuma sauran jami'an tsaro ne ke aikin tantance 'yan gudun hijirar da suka koma gida don tabbatar da ganin wasu mutanen daban ba su biyo cikinsu sun ɓad-da-sawu ba.

Ya ƙara da cewa Majalisar ƊInkin Duniya ta horas da jami'an kula da shigi da fice horo kan dabarun tantance 'yan gudun hijira ba tare da an cunguna musu ba.

Ya ce a kwanaki masu zuwa ƙarin 'yan gudun hijira kimanin dubu hamsin daga jamhuriyar Nijar da Kamaru za su koma ƙasarsu Nijeriya.

Labarai masu alaka