Buhari ya isa Abuja bayan da ya koma Nigeria

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Da sanyin safiyar Juma'a ne Buhari ya isa Najeriya

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya koma gida bayan shafe kwana 50 yana jinya a birnin London na ƙasar Ingila.

Shugaban ya sauka a wani filin jirgin sama na Kaduna, inda manyan jami'an gwamnatin jihar da kuma na tarayya suka tarbe shi.

Tuni kuma ya isa fadarsa da ke Abuja, babban birnin kasar, ta wani karamin jirgin saman soji.

Tun a ranar Talata 19 ga watan Janairu ne Shugaba Buhari ya tafi hutu da kuma ganin likita.

Daga bisani ya tsawaita hutun nasa, saboda abin da fadarsa ta ce, umurni ne na likitansa, domin yi masa gwaje gwaje da kuma buƙatar kara hutawa.

Hutun jinyar da kuma tsawaita shi da shugaban ya yi, sun janyo muhawara sosai a tsakanin 'yan kasar.

Tuni shugaban, mai shekara 74, ya gana da mataimakinsa, da wasu gwamnoni da kuma manyan jami'an gwamnatinsa.

Har yanzu babu cikakken bayani kan abin da ke damun shugaban Muhammadu Buhari amma jami'ansa sun nace cewa babu wani abin damuwa a cikin lamarin.

A ranar Alhamis ce mai magana da yawun shugaban Femi Adeshina ya sanar da cewa Muhammadu Buhari zai koma gida.

Sanarwar da ya fitar ta ce shugaban ya gode wa ɗaukacin al'ummar Nijeriya da ma na kasashen waje kan addu'o'in da suka rika yi masa da fatan alkhairi.

A baya-bayan nan wayar da ya yi da gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, lokacin da aka fara jin muryarsa tun bayan zuwa hutun jinyar, ya sa zuciyar 'yan ƙasar da dama kwanciya.

An yi ta ganin hotunan Muhammadu Buhari da wasu fitattun 'yan Nijeriya yayin ziyarar da suka riƙa kai masa lokacin da yake jinya a London.

Hakkin mallakar hoto Nigerian Government
Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugaba Buhari lokacin da ya dauki hoto tare da Shugaban darikar Angalican Archbishop na Canterbury, Justin Welby, dab da zai bar London.