Me ke kawo jinkirin bude makarantar nakasassu a jihar Nassarawa?

Gwamnan jiha Nassarawa Umaru Tanko Al Makura Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Gwamnatin jihar Nassarawar ta gina makarantar musamman saboda nakasassun yara don su samu ingantaccen ilmi

Wata makarantar zamani ta nakasassu da gwamnatin jihar Nassarawa a Nijeriya ta yi alkawarin budewa bana, har yanzu ba ta iya fara karatu ba.

A bara ne gwamnan jihar, Umaru Tanko Almakura, cikin shirin Ra'ayi-riga na sashen Hausa na BBC ya ce za a bude makarantar a bana.

Makarantar dai na kunshe ne da ginin azuzuwan nazare da firamare da kuma sakandare don bunkasa ilmin nakasassu.

Gwamnatin jihar ta ce ta gina makarantar ne musammam saboda yara nakasassu, kama daga makafi, da kurame da wadanda suka zamanto guragu tun suna yara, har ma da wadanda ke da lalurar kwakwalwa a wajen yara ko kuma autism.

Binciken da BBC ta yi, ya nuna cewa an kammala gina wannan makaranta, har ma an zuba kujeru a cikin azuzuwa.

Amma a wata hira, gwamna Almakura, ya bayyana dalilan da suka janyo samun jinkirin bude makarantar, a cewarsa dole sai an samu na'urori na zamani irin wanda kasashen da suka ci gaba ke tallafawa 'ya'yansu, 'yan makaranta wajen samun ilmi.

Ya kuma ce yanzu haka gwamnati ta yi odar wadannan na'urori, kuma nan da wata uku za su shigo don fara karatu a makarantar.

'' Abin damuwar shi ne wurin yara nakasassu idan ba a fara yi musu darasi tun suna yara da irin wadannan na'urorin da kuma hikima ta koyarwa ba, ba kasafai ake samun nasara da gaggawa ba''

'' Don haka za mu fara daukar yara daga shekara hudu a makarantar, inda za a kula da su, da abincinsu da wurin kwanansu, da za su yi karatu har zuwa matakin sakandare''.

Ana sa ran makarantar za ta samar wa yara nakasassu damar bunkasa karatunsu zuwa nan gaba.

Labarai masu alaka