An soma yunƙurin kawar da annobar shawara a Brazil

Kimanin mutum 130 ne aka tabbatar sun mutu Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Kimanin mutum 130 ne aka tabbatar sun mutu sakamakon cutar shawara a Brazil tun bayan watan Disamba.

Hukumomin Rio de Janeiro a Brazil sun bayyana aniyar yi wa daukacin al'ummar jihar riga-kafi, yayin da ƙasar ke fama da annobar shawara mafi muni cikin shekaru.

Ana buƙatar allurar riga-kafi miliyan 12 kuma gwamnati ta ce ta ƙuduri aniyar kammala aikin nan da ƙarshen shekara.

Ba a samu rahoton ɓullar shawara a jihar ta Rio de Janeiro ba, ko da yake, jihohi masu maƙwafta da ita ciki har da Espirito Santo da Sao Paulo na fama da cutar

Kimanin mutum 130 ne aka tabbatar sun mutu sakamakon cutar shawara a Brazil tun bayan watan Disamba, lokacin da aka fara gano ɓullarta.

Labarai masu alaka