Iraqi: An gano kabarin daruruwan mutane a gidan yari

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption A wannan mako dakarun gwamnatin Iraqi suka kwato Badush daga mayaka na IS

Mayakan sa-kai masu goyon bayan gwamnati a Iraqi sun ce sun gano wani katon kabari na jam'i mai dauke da gawawwakin daruruwan mutane wadanda kungiyar IS ta yi wa kisan gilla a kusa da birnin Mosul.

An gano kabarin ne a gidan yari na Badush wanda dakarun soji suka kwato daga mayaka na kungiyar IS a cikin 'yan kwanaki da suka gabata.

Kungiyar Hashed al-Shaabi, wadda ke wakiltar kungiyoyin mayaka na galibi 'yan Shi'a wadda ke cikin wadanda suka gano kabarin, ta ce ba ta kai ga tantance hakikannin adadin gawawwakin mutane dake cikin kabarin ba. Kungiyar ta ce daruruwan gawawwakin fursunoni fararen hula ne da kungiyar IS ta kashe a cikin gidan yarin.

To amma gano wurin ya zo daidai da abinda wani bincike da kungiyar kare hakkin bil-Adama ta Human Rights Watch ya tabo a 2014 inda sakamakon binciken ya ce kungiyar IS ta zattas da hukuncin kisa ga fursunoni da adadinsu ya kai 600 a gidan yarin.