Wani ya yi kutse a fadar gwamnatin Amurka

Image caption Donald Trump na yawan janyo cece-ku-ce

An kama wani mutum dauke da jaka a cikin fadar gwamnatin Amurka ta White House, kusa da kofar shiga gidan shugaban kasa dake cikin fadar, a cewar rahotanni.

Kafofin watsa labarai na Amurka sun ce wani dan-sandan ciki ne ya gano mutumin da ya yi kutsen a fadar Amurka jiya da misalin 12:00 na dare agogon Washington, wato yau da safe a kasashen Afirka.

Rahotannin sun kara da cewa shugaba Donald Trump na cikin gidan a lokacin da lamarin ya faru.

Kawo yanzu dai babu cikakken bayani kan manufar mutumin ta yunkurin shiga bangaren shugaban kasa a cikin fadar Amurkar.

Ba a kuma yi karin bayani ba kan ko wane ne mutumin. An dai bincika jakar mutumin ba a samu wani makami ba.

To sai dai shugaba Trump ya yaba wa jami'an tsaron fadar gwamnatin saboda yadda suka dakile mutumin tun kafin ya yi wani abu na cutarwa, kana ya bayyana mai kutsen a matsayin mutum mai ''neman tayar da zaune tsaye.''