Malamai za su shiga sabon yajin aiki a Nijar

Image caption Shugaba Muhammadou Issoufou na fuskanatar matsin lamba yayin da jamhuriyar Nijar ke ci gaba da kasancewa cikin kasashe mafiya talauci da koma-baya a harkar ilimi.

A jamhuriyar Nijar kawancen kungiyoyin malaman makaranta na CAUSE Niger da SYNACEB sun ayyana cewa za su fara yajin aiki na kwanaki biyar daga ranar Litinin ta tafe.

Sun ambata hakan ne yayin da wani yajin aikin nasu na kwanaki biyar ke karewa.

Malaman makarantun wadanda akasari na firamare ne, na kukan cewa gwamnati ta kasa cika wasu alkawurra na kyautata masu yanayin aiki da alabshi bayan da suka kulla wata yarjejeniya a baya tare da ita.

Amma gwamnatin Nijar din ta ce babu wasu alkawullan da ba ta cika ba cikin wadanda ta dauka. Gwamnatin ta ce ta kammala biyan basussukan albashi kuma ta na ci gaba da biyan albashin malaman makarantun a kan kari.

Ministan Ilmin Kimiya da Fasaha, Alhaji Tijani Abdulkadiri, ya shaida wa BBC cewa kungiyoyin malaman ba su la'akari da muradun kasar illa muradun kansu.

To sai dai malaman na cewa gwamnatin ta kasa cika alkawarin da ta yi masu na karin albashi don haka za su koma yajin aiki sai bukata ta biya. Gwamnatin kasar na cewa tana gudanar da bincike kan nagartar malaman domin tabbatar da ko sun cancanci su yi aikin koyarwa ko kuma ba su cancanta ba.

Kungiyoyin malaman sun yi watsi da shirin gwamnatin na tantance malamana makarantun na Firamare da kuma ikirarin da ta ke yi na cewa babu isassun kudade da za a yi masu karin albashi.