Bola ta yi ajalin mutum 48 a Habasha

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Bidiyon yadda 'yan sanda da masu aikin agaji ke ceto a wajen

Akalla mutum 48 ne suka mutu a wajen birnin Addis Ababa babban birnin kasar Habasha wato Ethiopia, sakamakon zabtarewar kasa a wani babban wurin zubar da shara wanda ake amfani da shi tun kimanin shekara hamsin da ta gabata.

Jami'ai sun ce har yanzu ba a gano gomman mutane ba tun bayan da al'amarin ya faru a ranar Asabar da daddare. Wani ganau ya ce kusan mutum 150 ne ke wajen a lokacin da abin ya faru.

Ana ci gaba da aikin ceto yayin da rahotanni ke cewa ba a ji duriyar mutane da dama da lamarin ya rutsa da su ba amma ma'aikatan agaji sun zakulo gawawwakin mutane masu yawa.

Ana dai fargabar cewa laka da tarin bola ce ta binne wasu daga cikin dimbin mutanen da ba a gansu ba.

Tabo da sauran tarkace sun kuma binne wasu gidaje na wucin gadi da ke kusa da inda bala'in ya faru.

Cikin wadanda lamarin ya shafa akwai wadanda ke ayyukan tsince-tsince a babban jujin domin neman samun abubuwa masu sauran amfani da za su iya sayarwa don su ci da iyalansu.

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption An shiga makoki a Habasha

Akwai kuma dumbin yara da su ma ake zaton suna karkashin tarin bolar.

Wani mazaunin yankin Musa Sulaiman ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa, ya ji wata kara sai kuma ya ga guguwa ta turnike wajen ta yo kansu gadan-gadan a lokacin da zaftarewar kasar ta afku.

Tebeju Asres kuwa cewa ya yi tuni zaftarewar kasar ta lakume gidansu.

"Mahaifiyata da 'yan uwana mata uku suna wajen loakcin da lamarin ya faru. Yanzu haka ban san ina suke ba," ya shaida wa AFP.

Wakilin BBC ya ce daruruwan mutane ke neman tsince-tsince a bolar da su sayar su sami na rufin asiri, inda wasu su ma suke zaune din-din-din a wajen.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An fi shekara 50 ana tara bola a wannan yanki

Hukumomi suna gina wani kamfani da za a dinga samar da makamashi ta hanyar amfani da bola.

Suna shirin fara kona bolar da ake tarawa a birnin, wanda ke da yawan mutane kusan miliyan hudu, don mayar da bolar hanyar samar da wutar lantarki.

Image caption Habasha na daya daga cikin kasashen yankin gabashin Afirka