Sarkin saudiyya na ziyara a Japan

King salman
Bayanan hoto,

Sarkin Saudiyya na samun tarba ta kasaita a kasashen Asiya

Sarki Salman na Saudiyya ya sauka a Tokyo a wata ziyara da ita ce irinta ta frako da wani sarki na Saudiyya ya kai kasar Japan cikin kusan shekaru hamsin.

Rahotanni na cewa an tanadi dakunan kasaita fiye da 1000 a otel-otel domin sama wa dimbin 'yan tawagar sarkin na Saudiyya masauki. An kuma tanadi daruruwan motocin alfarma na Limousines.

Japan na fatan amfani da ziyarar wajen karfafa huldarta da kasar Saudiyya, kana ta taimaka wa Saudiyyar wajen fadada tattalin arzikinta wanda ya dogara sosai a kan man fetur.

Sarki Salman dai na rangadi ne a yankin Asiya. Tuni ya ziyarci kasashen Indonesiya da Malesiya kuma ana sa ran zai wuce zuwa kasar Sin.