Masu kitso za su fara gano tabon cin zarafi a kan mata

Salon dresser
Image caption Shirin horas da masu gyaran gashin zai karfafa gwiwar mata su rika ba da rahoton musgunawar da abokan zamansu suka yi musu

Ana horas da masu gyaran gashi don gano alamun da ke nuna ko abokan zaman waɗanda suke yi wa kitso sun musguna musu.

Wata mai gidan gyaran gashi Beau salon a yankin Norwich cikin Burtaniya ce ta bijiro da wannan tunani, bayan ta gano wata doka da ake ƙoƙarin ɓullo da ita a Amurka wadda ta buƙaci a riƙa bai wa masu gyaran gashi irin wannan horo.

Rachel Buck, wadda ke aiki da wata gidauniyar agaza wa matan da abokan zamansu suka musgunawa mai suna Leeway, ta ce ba wai ana buƙatar masu gyaran gashi suka zama 'yan magori ba ne, ana muradin su ƙarfafa gwiwar masu zuwa kitso ta yadda za su nemi tallafi.

Ta ce "Lokacin da na ga Illinois ta tsaida wata muhimmiyar shawara don shawo kan musguna wa abokan zama, sai na ce wannan kyakkyawar dama ce mu koyi darasi."

Helen Burrows ta gidauniyar Leeway, ta ce: "Mafi hatsarin lokacin da ake samun musguna wa abokan zama na faruwa ne ana daf da rabuwa.

"Don haka masu gyaran gashi za su iya tallafa wa irin waɗannan mutanen, ta hanyar yi musu bayanin cewa wannan lokaci mai hatsari kuma za a iya samun mafita."

Labarai masu alaka