Me ke gaban Buhari bayan komawa aiki?

Buhari Hakkin mallakar hoto Nigerian Government
Image caption Shugaba Muhammadu Buhari ya ce bai taba irin ciwon da ya sa shi tafiya London ba

A ranar Litinin ne shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, ya koma bakin aiki a fadar gwamnati ta Aso Rock da ke babban birnin kasar Abuja.

Shugaba Buhari ya shiga ofishinsa ne da misalin karfe 10:45 inda daga bisani shugaban ma'aikatan fadar, Malam Abba Kyari da mai ba shi shawara kan harkar yada labarai, Femi Adesina da kuma mai magana da yawun shugaban kasar, Garba Shehu suka shiga ofishin shugaban kasar.

Femi Adeshina ya wallafa a shafinsa na Twitter cewar shugaba Buhari ya rattaba hannu kan wasikar da ke sanar da Majalisar Dokokin Kasar cewar shi ya koma bakin aiki.

Rahotanni sun ce tuni mataimakinsa Yemi Osinbajo, wanda ya rike ragamar kasar a lokacin da shugaban yake jinya a London, ya yi masa bayanin yadda abubuwa suka wakana da baya nan.

Tuni wannan batu ya mamaye shafukan sada zumunta da muhawara na Najeriya, inda wasu ke murnar komawar shugaban bakin aiki, yayin da wasu kuwa suke ganin har yanzu ba shi da cikakkiyar lafiyar da zai ci gaba da rike kasar.

A binciken da BBC ta yi a shafin Twitter ta gano yadda wani shafi mai suna The Nigerian Wailers‏ @NGRWailers, ya rubuta cewa,"Idan kun san Buhari ko kuma kuna da alaka da shi, to ku gaya masa ba hutu kawai yake bukata ba, gara kawai ya yi murabus. Ta haka ne kawai zai iya tunkarar matsalar lafiyarsa."

Wannan shafi dai har ya yi amfani da wani maudu'i mai taken #BuhariResignNOW.

Sai dai a hannu guda kuma akwai dumbin masu murnar gain wannan rana ta komawar shugaba Buhari bakin aiki, inda suke ta yi masa fatan alheri da kuma fatan ya Allah ya ba shi cikakkiyar lafiyar ci gaba da ayyukan da suka dace.

Amma wasu kuwa na ganin akwai manyan kalubale da suke gaban shugaban wadanda zai yi wuya ya shawo kansu duba da yanayin lafiyar tasa.

Hakkin mallakar hoto NIGERIAN GOVERNMENT
Image caption An yi ta fitar da rahotanni da ke nuna samun baraka tsakanin shugaban da mataimakinsa

Ga dai kadan daga cikin wasu sakonni da wasu suka rubuta a shafin BBC Hausa Facebook:

Zira V Kwada Usma: "Ni a nawa ra'ayi kamata ya yi shugaba Muhammad Buhari, ya tabatar da ya samu cikakkiyar lafiya, kafin ya koma bakin aiki. Duk wanda ba ya goyon bayan Buhari ya samu cikakkiyar lafiya kafin ya kuma bakin aiki, to fa makiyinsa ne, ba ya sonsa. Amma in ya gani zai iya, to fatanmu shi ne Allah ya taimaka."

Rilwanu Sa'idu Gayari: "Muna fatan Allah ya ba shi ikion ci gaba da mulkinsa cikin tsanaki da taimakon Allah."

Aliyu Abdulqadiri: "Ni kam tausayinsa nake ji wallahi. Ga tsufa ga lalurar jiki ga dumbin matsalolin kasar nan ga dumbin masu zagon kasa. To sai mu ce Allah ya agaza masa."

Gomna James: "Nawa ra'ayin shi ne gara Baba ya nemi hutu ya koma. Ina dalilin sauri a cikin al'amarin nan."

'Kalubale'

Masu sharhi na ganin a yanzu 'yan Najeriya sun zura ido domin ganin tunda shugaba Buhari ya koma bakin aiki, ko zai ci gaba da matakan da mataimakinsa Yemi Osinbajo ya dauka a lokacin da baya nan da kuma kara fitar da wasu matakan na farfado da tattalin arzikin kasa.

Wani masanin siyasa Dakta Abubakar Kari, ya ce, "Za a zuba wa shugaba Buhari ido don ganin yadda zai ci gaba da yaki da almundahana bayan ya wanke sakataren gwamnatinsa, Babachir David Lawal, daga zargin cin hanci da rashawa kafin ya tafi London jinya."

Dakta Kari ya kara da cewa, ana sa ran shugaban zai kara kaimi wajen aiwatar da kasafin kudin bara wanda har yanzu ba a gama aiwatar da shi ba, a yayin da ake jiran tabbatar da dokar kasafin kudin bana wadda Majlaisar Dokokin kasar za ta yi a wata mai zuwa.

Ya ce, an kuma zuba ido a ga yadda shugaban Najeriyar zai ci gaba da tattaunawa da tsagerun 'yan Neja-Delta domin samun dawwamammen zaman lafiya a yankin mai arzikin man fetur.

"Akwai kuma kudurorin da ya kamata shi shugaban Najeriyar zai rattaba wa hannu domin su zama dokoki," in ji Dakta Kari.

A wata hira da BBC mai bai wa shugaban shawara kan harkokin yada labarai Malam Garba Shehu, ya tabbatar da cewa shugaba Buhari zai ci gaba da aiki da kyawawan manufofinsa kamar yadda da ma can yake yi.

Haka kuma wasun 'yan Najeriyar za su so su ga yadda shugaban zai yi da cece-kucen da ya barke tsakanin shugaban hukumar yaki da fasa kauri na kasar, Kanar Hameed Ali mai Ritaya, da Majalisar Dattawan kasar kan yunkurin hukumar Custom na fara karbar harajin shigar da mota daga masu motoci.

Shugaba Buhari dai shi ya nada Kanar Hameed Ali wanda na hannun damansa ne a matsayin shugaban hukumar.

A ranar Juma'ar da ta gabata ne dai shugaba Buhari ya dawo Najeriya bayan ya shafe kwana 50 yana hutun jinya a London, al'marin da ya jawo ce-ce-ku-ce a kasar, har wasu na zargin cewa ya mutu ne.

Labarai masu alaka