Nigeria: Ana gudanar da bincike kan rikicin Ile-Ife

IG Hakkin mallakar hoto Idris Kpotun Facebook
Image caption Sifeton 'yan sanda Idris Ibrahim Kpotun ya tura tawagar ne don gano me ya jawo fadan

Tuni wata tawaga da sifeto janar na 'yan sandan Najeriya ya kafa ta isa garin Ile-Ife a jihar Osun, da ke Kudu maso Yammacin kasar, domin fara gudanar da bincike kan wani rikicin kabilanci da ya barke makon da ya gabata.

A ranar Larabar da ta gaba ce rikicin kabilanci ya barke a tsakanin Hausawa da Yarbawa - a sakamakon gardamar da ta taso tsakanin wata mace Bayarba da kuma wani Bahaushe.

Rahotanni dai na cewa an samu salwantar rayuka kusan 40 da dukiya mai yawa.

Kwamitin dai zai gudanar da binciken ne a karkashin Hammed Bello.

Wakilin BBC ya ce tuni tawagar ta dukufa akan gudanar da bincike, inda ta fara zagayawa da kuma yin zama da shugabannin al'umma don lalubo hanyoyin dakile duk wani yunkurin tashin hankali irin na kabilanci a garin na Ile-Ife.

Kwamishinan 'yan sanda mai riko a jihar osun, DCP Aminu Koji, ya tabbatar da isar tawagar inda ya ce, "Tana nan a Ife ai, don yin bincike, za ta duba menene ya faru, me ya kawo ga wannan - kawai wannan marin ne ko kuma dai wani abu ne daban.

Tun a ranar Lahadi ne dai aka yi jana'izar a kalla mutum 36 a Osogbo, babban birnin jihar, kamar yadda sarkin Hausawan Ile Ife Alhaji Abubakar Mahmuda Madagali ya shaida wa BBC.

An dai yabawa yadda al'ummar Arewacin kasar ta kai zuciya nesa, wani lamari da masu kula da al'amura ke cewa wannan ya isa a gudanar da binciken ke-ke- da ke-ke domin hukunta duk wasu da aka samu da hannu a kisan mutanen da basu ji basu gani ba.

A nata bangaren, gwamnatin jihar Kaduna ta yi gargadi ga mutanen jihar da su guji yada bidiyo da hotunan abin da ya faru a Ife din don gudun tunzura mutane su dau doka a hannunsu.

A wata sanarwa da mataimakin gwamnan Kaduna ta fuskar yada abarai Samuel Aruwan, ya ce za a dauki matakin ladabtarwa kan duk wanda aka samu da yada irin wannan abu don neman tayar da wata fitinar daban.

Rikicin kabilanci a Najeriya dai ya zama ruwan dare ga al'ummar kasar, kuma sau da yawa su kan dauki doka a hannu.

Bincike ya nuna cewa akasari daga rikicin da ke tasowa musabbabinsa bai taka kara ya karya ba - kuma al'amari ne da za a iya warware shi idan an kai zuciya nesa.

Labarai masu alaka