Ba mu hana PDP ganin Buhari ba — APC

Shugaba Najeriya Muhammadu Buhari ya dawo gida bayan dogon lokacin da ya shafe a London ana duba lafiyarsa Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaba Najeriya Muhammadu Buhari ya dawo gida bayan dogon lokacin da ya shafe a London ana duba lafiyarsa

Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta musanta zargin da babbar jam'iyyar adawar kasar, wato PDP ke yi cewa APC ce ta katse mata hanzari a kokarinta na zuwa Ingila domin duba lafiyar shugaba Muhammadu Buhari.

Sakataren jam'iyyar APC na kasa, Alhaji Maimala Buni, ya shaida wa BBC cewa, "Jam`iyyarmu ba ta da alaka da hanyar da ake bi wajen ziyartar shugaban kasa, neman magana kawai PDP ke yi."

Alhaji Maimala Buni ya ce batun zuwa duba shugaban kasa ba abu ne na siyasa ba, ballantana a zarge su da da yin wani abu domin su hana.

Sakataren jam'iyyar, ya ci gaba da cewa, "Gutsuri tsoma kawai PDP ke yi, amma abin da shugaban Najeriyar ya fi bukata shi ne addu'a kamar yadda sauran 'yan kasa ke yi masa."

Me ke gaban Buhari bayan komawa aiki?

Shugaba Muhammadu Buhari ya kwashe kimanin kwanaki 50 a Ingila wajen neman magani.

Wasu masu fada aji da suka hada da shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Bukola Saraki da kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara, duk sun yi takakkiya zuwa birnin London domin duba shugaban.

'Yan Najeriya Musulmai da Kiristoci sun ta faman yi wa shugaban addu'o'in neman lafiya.

Labarai masu alaka