Arsenal da Manchester City za su kece raini

Wannan ne karon farko da Manchester City ta kai ga zagayen kusa da na karshe a gasar kofin FA
Image caption Wannan ne karon farko da Manchester City ta kai ga zagayen kusa da na karshe a gasar kofin FA

Abokan hamayya na birnin London wato Chelsea da Tottenham za su buga a wasan kusa da na karshe a gasar cin kofin FA, bayan da Chelsea din ta fitar da Man U a wasan a jiya litinin.

Ita kuwa Arsenal wadda wannan ne karo na ashirin da tara da zata buga wasan kusa da na karshe na kofin FA, za ta kara ne da Manchester City.

Za a yi dukkan wasannin biyu a Wembley a ranakun 22 da 23 ga watan Aprilu.

Chelsea ta yi nasarar fitar da Manchester United ne da ci 1-0, yayin da ita kuma Arsenal ta ci Millwall a ranar Lahadi.

Arsenal wadda ta ci kofin a shekarun 2014 da 2015 ta yi rawar gani a wasan da ta buga.

Wannan ne dai karon farko da Manchester City za ta buga wasan kusa da na karshe a kakar wasanni hudu, bayan ta lallasa Middlesbrough da ci 2-0.

Labarai masu alaka