Shin masu 'ya'ya sun fi tsawon rai?

. Hakkin mallakar hoto .
Image caption .

Wani bincike a kasar Sweeden wanda ya bibiyi kusan mutum miliyan daya da rabi, ya nuna cewa masu 'ya'ya sun fi dadewa a duniya.

Masana kimiyya sun dubi tsawon rayuwar mata da maza wadanda aka haifa tsakanin shekarar 1911 da kuma 1925, kuma suka gano cewar wadanda suke da akalla da daya sun fi wanda bai haifi da ko daya ba sa rai da doguwar rayuwa.

Binciken ya gano cewar a bambancin yiwuwar rayuwa tsakanin mata da maza shi ne shekara biyu ga maza a lokacin da mata ke da shekara daya da rabi.

Binciken ya nuna cewar iyaye za su iya amfana da tallafi daga 'ya'yansu idan sun tsufa.

Karin Modig da abokan aikinta sun yi amfani da alkaluman kasar Sweden mai dauke da sunayen mutanen kasar domin su gano tsawon rayuwar tsoffin mutane fiye da miliyan 1.4, dangane da ko sun yi aure ne ko ba su yi ba, da kuma ko suna da 'ya'ya ko basu da su.

Masu binciken sun ce binciken shi ne irin sa na farko da ya nemi sanin ko akwai alaka tsakanin tsawon rayuwa da kuma haihuwar 'ya'ya.

Idan aka yi la'akari da dalilai masu tasiri irin su ilimi, bambancin barazanar mutuwa na karuwa da yawan shekaru tsakanin iyaye da marasa yara.

Alal misali, maza 'yan shekara 90 da ba su da 'ya'ya, suna fuskantar barazanar mutuwa da kashi 17.7 cikin 100 inda mazaje masu irin wannan shekaru irin nasu wadanda suke da yara ke fuskantar barazanar mutuwa kashi 16.2 cikin 100.

Miss Modig ta ce an shirya yin wani binciken da zai biyo bayan wannan, don gano tasirin wadannan batutuwa, inda za a fayyace su sosai.

Binciken ya yi nazari a kan bayanan da aka tattara na maza 704,481 da mata 725,290, wadanda aka haifa tsakanin shekarun 1911 da 1925, wadanda ke zama a Sweden.