Bankuna na neman masu sayen dala 'ruwa a jallo'

CBN
Image caption A baya-bayan nan ne CBN ya dauki matakin wadata bankunan kasar da kudin kasashen waje

Bankuna a Najeriya na neman mutanen da za su sayi dala ruwa a jallo, inda suka ce a yanzu suna da kudaden kasashen wajen da dama da babban bankin kasar CBN, ya basu.

Masu sharhi da dama na ganin tun da a yanzu bankuna na 'neman kai' da kudaden kasashen wajen, hakan na iya daga darajar Naira, ya kuma rage wawagegen bambancin da ke tsakanin musayar dala da naira a kasuwanni bayan fage da bankuna.

Najeriya dai tana fama da matsalar rashin isassun kudaden kasashen waje, al'amarin da ya jawo hauhawar farashin kayayyaki da tsadar rayuwa ga 'yan kasar.

Wanne siddabaru CBN ya yi?

Wani darakta a CBN Isaac Okoroafo, ya shaida wa BBC cewa an samu saukin halin da kasar ta shiga ne tun bayan da babban bankin ya fara aiwatar da wani sabon tsari na samar da kudaden waje ga bankuna.

Ya ce, "A cikin fiye da makonni biyu da suka gabata, mun bayar da dala biliyan 1.2, ga wadanda aka ba su canji kai tsaye, wasu kuma ake bayar wa ga masu biyan kudin makaranta da na asibiti da sauran bukatun matafiya."

BBC ta kai ziyara kasuwar masu musayar kudi ta bayan fage da ke unguwar Wuse a Abuja, babban birnin Najeriya, ta kuma ga yadda wadatar dala a bankuna ta sa farashinta ke ci gaba da saukowa.

"Gaskiya mu muna farin cikin hakan, mu mun fi son ci gaban kasa, don haka ba mu ki ma dalar ta dawo 170 ba," in ji Alhaji Rabi'u Gada, wani dan canji.

Ya kara da cewa banki na sayar musu da dalar a kan naira 381 su kuma suna sayarwa a kan 399.

Yayin da babban banki kuwa ke sayarwa bankuna a kan 315.

Alhaji Gada ya ce, "Hakan kuma bai hana mu ma mu samu abokan ciniki ba sosai, don ko a yau ba zan iya kirga yawan wadanda suka zo nan ba."

Faduwar farashi

A hannu guda kuma, hukumar kididdiga ta kasa NBS, ta fitar da wani rahoto da ke cewa 'farashi' ya sauka sosai a Najeriya, inda hakan ke nuna cewa tattalin arzikin kasar ya fara farfadowa.

Hukumar NBS ta ce hauhuwar farashin ya sauka daga kashi 18.72 cikin 100 da yake a watan Janairu zuwa kashi 17.78 cikin 100 a watan Fabrairun 2017.

Duk da raguwar farashin, adadin hauhawar farashi yana nan a matakin da yake, wanda shi ne mafi yawa tun zamanin mulkin shugaba Olusegun Obasanjo.

Labarai masu alaka