'Ana sanya wa Kifi maganin adana gawa a Ghana'

Bushashshen Kifi na da farin jini a Ghana Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Bushashshen Kifi na da farin jini a Ghana

A kasar Ghana, masu siyar da busasshen Kifi da aka fi sani da koobi na garin Yaa -ji da ke yankin Brong Ahafo, sun yi barazanar shigar da ministan muhalli da kimiyya da fasaha na kasar kara bayan wasu kalamai da ya yi dangane da kifin da su ke sai da wa.

Ministan ya zargi masu sayar da Kifin da amfani da wani sinadari mai hadari da ake kira Fomalin wajen adana Kifin na su.

Shi dai sinadarin Fomalin, ana mafani da shi ne wajen adana gawa idan ana so ta jima kafin a binne ta.

Wannan zargi da ministan ya yi wa masu sayar da kifin ya bar baya da kura, in da masu sayar da Kifin ke cewa wannan kalamai na minista ya kashe musu kasuwa, dan haka za su kai karar sa gaban kuliya.

Sannan kuma sun musanta cewa suna amfani da sindarin Fomalin din wajen adana Kifinsu.

Busashen Kifin da ake kira Koobi dai na da farin jini ga mutanen kasar ta Ghana.

Ana dai iya ajiyar Kifin zuwa lokaci mai tsawo idan an sanya abin da zai hana shi lalacewa da wuri.

Labarai masu alaka