Za a cire Venezuela daga OAS

Venezueala ta zargi Mr Almagro da yi mata bita da kulli
Image caption Venezueala ta zargi Mr Almagro da yi mata bita da kulli

Sakatare janar na kungiyar kasashen yankin Amurka ya yi kira ga mambobin kungiyar da su dakatar da Venezuela daga kungiyar, har sai ta sanar da lokacin gudanar da zabe a cikin kwana 30.

Luis Almagro ya ce gwamnatin shugaba Nicolas Maduro ta yi watsi da sakamakon zaben 'yan majalisun dokokin kasar da aka yi a shekarar 2015, sannan ta kuma sanya abokan adawa a gidan kaso, wanda hakan ya sabawa tsarin dimokradiyyar kungiyar.

Har yanzu dai shugaba Maduro na Venezuela bai ce komai ba a kan sanarwar sakataren kungiyar, sai dai kuma a baya ya zargi Mr Almagro da bin umarnin gwamnatin Amurka da kuma kokarin ware kasarsa.

Dole sai kaso biyu bisa uku na kungiyar kasashen yankin Amurkan ya amince da bukatar Mr Almagro, sannan a dakatar da Venezuela daga kungiyar.

Labarai masu alaka