Kayan agaji sun isa wasu yankunan Syria

Kusan mutum dubu 60 ne ke bukatar kayan agaji a yankunan da aka yiwa kawanya a Syria Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Kusan mutum dubu 60 ne ke bukatar kayan agaji a yankunan da aka yiwa kawanya a Syria

Kungiyar agaji ta kasa da kasa ta Red Cross tare da Majalisar Dinkin Duniya sun ce ayarin da ke dauke da kayan agaji ya isa garuruwa hudu wadanda aka yiwa kawanya a Syria domin kai kayan agaji ga mutanen da ke ciki da yawansu ya kai dubu 60.

Wannan shi ne karon farko da za a kai kayan agaji ga wadannan mutanen tun watan Nuwambar bara.

Kungiyar ta Red Cross ta ce kayayyakin agajin sun isa Madaya da Zabadani da kuma wajen garin Damascus wanda dakarun gwamnati suka yiwa kawanya.

Sauran garuruwan su ne Foua da Kafraya a lardin Idlib wanda 'yan tawaye kuma suka yiwa kawanya.

Da farko dai sai da jami'in kula da kayan agaji na Majalisar ta Dinkin Duniya a Syria, Kevin Kennedy ya ce babu wani ayari ko da guda daya da ya samu damar kai irin wannan agaji ga garuruwan a watan jiya.

A wani bangaren kuma, wani bincike da mujallar The Lancet ta gudanar ya nuna cewa an mayar da harkar lafiya wani makami na yakar jama'a, a Syria.

Wadanda suka gudanar da binciken sun ce gwamnatin Syria da babbar kawarta Rasha ne ke amfani da irin wannan dabara wajen tursasa mutane su bi turbar da suke kai.

Mujallar ta kuma yi gargadin cewa tursasa mutane saboda bukatar da suke da ita ta magani ta hanyar hana su samun maganin, wani abu ne mai munin gaske.

Haka kuma mujallar ta ce al'amarin barazana ne ga dokar kasa da kasa ta agaji wadda ta bai wa kowa damar samun magani ba tare da nuna banbanci ba.

Labarai masu alaka